‘Yan sanda sun kama ma’aurata bisa zargin kwarawa maƙociya tafasasshen ruwa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan sanda a jihar Ebonyi sun cafke wasu ma’aurata, Chigozie da matarsa, Ginika, bisa zarginsu da kwarawa makwabciyarsu mai suna Cynthia Ucha tafasasshen ruwa, a titin Akidi a Abakaliki, babban birnin jihar.

A cewar shaidun gani da ido, lamarin ya fara ne daga cacar-baki tsakanin Ginika da Cynthia, lamarin da ya rikide ya zama faɗa har da doke-doke.

Wani ganau mai suna Ozioma ya baiyana cewa Chigozie tare da ‘ya’yansa da kuma surukansa sun shigar wa Ginika fadan tare da cin zarafin matar.

Ozioma ya ƙara da cewa a baya ma’auratan sun yi wa bazawarar barazana a lokuta da dama.

Ozioma ya ce “Tun da ta dawo gidan da zama ta tsare kanta kuma ta yi kokarin kaucewa rikici.” “Amma maimakon a kyale ta ta zauna lafiya, Ginika da danginta sun sa mata tsama har ta kai ga ba za ta iya jurewa ba.”

Bayan afkuwar lamarin, tun da farko an tsare wadanda ake zargin a babban ofishin ‘yan sanda, inda daga bisani aka mika su zuwa sashin kula da makamai da dabaru (SWAT) da ke hedikwatar ‘yan sanda da ke Abakaliki.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi, SP Joshua Ukandu, ya tabbatar da kamun, ya kuma bayyana cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

By ukarofi