Mai Kanuri na Legas ya naɗa sabbin muƙamai a fadarsa

Spread the love

Daga TANIMU AHMED a Legas

Mai girma sarkin Bare-barin Legas Mai Kanuri Alhaji Mele Abaca ya naɗa ƙarin hakimai da Zanna a fadarsa da ke unguwar Ijora a jihar Legas a ranar Lahadi da ta gabata. 

Bikin ya samu halarta mutane da dama da suka hada da masu riƙe da sarautun gargajiya na Hausawa da Arab da kuma sauran jagororin Hausawa daga ciki da wajen Legas domin taya murna ga waɗanda aka nada wa sababbinn muƙaman na Zanna da kuma Hakimai.  

Duka dai waɗannan mukamai bai wa mutanen da suka fito ne daga yanki Ajeromi na ƙaramar hukumar Ajeromi Ifelodun na jihar. 

Mai Kanurin na Legas Alhaji Mele Abaca ya yi kira ga wadanda aka yi wa nadin da su kasance jagori nagari da kuma kulla kyakkyawar dangantaka da mutanen da suke ƙarƙashinsu. 

Ya ce ‘’Ina kira ga wadannnan mutane da Allah Ubangiji Ya sa suka samu wannan mukami na zanna da kuma Hakimai da su kasance masu gaskiya da riƙon amana da kuma kwatanta yin adalci a tsakanin mutanen da suke jagoranta, kada su yi zalinci ko kuma musguna wan a kasa da  su. Su sani cewa Allah Ubangiji ne ya zabe su a wannan mukami da suka samu, a saboda haka ina mai jaddada kira a gare su da rike amanar da Allah Ubanjigi Ya dora musu.’’ 

Mai Kanurin ya kuma buƙaci matasa da su kama sana’a domin ta hanyar sana’a ce kadai za su tasre mutuncinsu a idanun al’uma kana kuma su guji mu’amala da miyagun kwayoyi, su kuma kasance masu bin doka da oda a duk inda suka samu kansu. 

A ƙarshe kuma ya yi kira ga mutane das u zauna lafiya da junansu ba tare da tashin hankali ba. Zanna Ibrahim Mustafa sakatare a fadar sarkin bare-bari na Legas ya taya waɗanda aka naɗa a wannan sababbin muƙamai tare da yin kira a gare da su kasance masu juriya ga duk wani ƙalubale da za su iya fuskanta, kasancewar harka da jama’a tana bukatar hakuri, ya kuma taya su murna tare da yi musu aduwar fatan alheri.

Zannan Ibrahim Mustafa ya ce ‘’Babu shakka wannan nadi da aka yin a zanna da kuma hakimai ga mutanen Ajeromi zai kara hada kan duk wani dan Arewa da ke nan Legas ba ma kawai Kanuri. Tabbas mai martaba sarki bai yi zaɓen tumun dare ba.’’ 

Alhaji Modu Kofa wanda ke zaune a Hausa Layi Ajeromi wanda shi ma aka bai wa sarautar Ajiya a fadar sarkin ya nuna farin cikinsa tare da yin godiya ga Allah bisa wannan sabon nadi da aka yi masa tare da kira ga ‘yan uwansa da suka samu wannan muka da su haɗa ƙarfi da ƙarfe wuri daya wajen kawo hadin kai a tsakanin ‘yan Arewa mazauna jihar Legas da ma Nijeriya baki ɗaya. 

Ya ce a madadin ‘yan uwana da aka yi mana wannan naɗi tare muna gode wa Allah da cikin ikonsa Ya sa mai martaba ya ba mu waɗannan mukamai, mu uku ne aka yi wa nadin, ni an nada ni mukamin Ajiya na Ajegunle Ajeromi, sai kuma sauran ‘yan uwana da aka yi mana nadin tare wadanda su aka yi musu nadin zanna wato Alhaji Abubakar Zanna da Alaji Sharif Mele. 

“Gaskiya mutane sun  nuna mana kauna bisa wannan mukamai da muka samu, muna yi wa kowa fatan alhaeri, Allah Ya kai kowa gida lafiya.’’ 

Waziri a fadar sarkin Bare-barin na Legas Alhaji Ibarahim wanda kuma shi ne sarkin Hausawa na yanki Aja bakiɗaya ya taya waɗanda suka samu wannan mukamai das u rike gaskiya da rikon amana.

‘’Ina kira ga wadanda Sarki ya yi wa waɗannan nade-nade da su riƙe amanar da Allah Ubangiji Ya dora musu, su kuma kasance jakadu na ƙarfafa haɗin kai a tsakanin dukannin ‘yan Arewa mazauna Legas da ma Nijeriya baki ɗaya’’ a cewar shi. An dai gudanar da bikin naɗin sarautar da aka yi ciki farin ciki ba tare da tashin hankali ba.

By ukarofi