Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Maryam Abacha, matar Marigayi Janar Sani Abacha, tsohon shugaban soja na Nijeriya, ta ce mijinta ya ajiye wa Nijeriya kuɗi, amma aka wawashe su bayan rasuwarsa.
A wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin na TɓC, wacce jaridar TheCable ta rawaito, Maryam ta buƙaci a kawo hujja da ke nuna cewa mijinta ya ɓoye kuɗaɗen sata a ƙasashen waje.
Abacha ya mulki Nijeriya a matsayin shugaban soja da kuma kwamandan rundunar sojin ƙasa daga 1993 zuwa 1998, kafin rasuwarsa a ranar 8 ga Yuni, 1998.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta ƙwato wasu kaso-kaso na kuɗaɗen da ake zargin Abacha ya ɓoye a bankunan ƙasashen waje.
A cewar rahotanni, daga shekarar 2020, an ƙwato sama da dala biliyan 3.624 daga cikin kuɗaɗen da Abacha ya ɓoye.
“Wa ne shaida na kuɗaɗen da ake cewa an ɓoye?” inji Maryam.
“Ka ga hannu ko shaida cewa kuɗin na waje ne? Kuma kuɗin da mijina ya adana wa Nijeriya, cikin ‘yan watanni sun bace. Babu wanda ke magana a kan hakan.”
Ta ce yadda ake ci gaba da zargin mijinta alamar wani mummunan hali ne da ke addabar al’umma.
“Me ya sa kuke ɗora wa wani laifi? Ko ƙabilanci ne ko bambancin addini ne ko me ke damun ‘yan Nijeriya?” inji ta.
