SERAP ta buƙaci Tinubu ya dakatar da Wike rufe ofisoshin jakadanci 34 a Abuja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Nijeriya, ta buƙaci shugaba Bola Tinubu ya bai wa ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike umarnin janye barazanar da ya yi na rufe ofisoshin jakadancin ƙasashen waje 34 a Abuja.

Martanin ƙungiyar na zuwa ne bayan da hukumar kula da babban birnin tarayya FCTA, ta ce ana bin aƙalla ofisoshin jakadanci 34 kuɗin haya tun 2014.

Ofisoshin jakadanci da abin ya shafa sun haɗa da na Ghana, Thailand, Eƙuatorial Guinea, Côte d’Iɓoire, Rasha, Philippines, Netherlands, Turkiyya da Guinea, Ireland, Uganda, Iraƙi, Zambiya, Tanzaniya, Jamus, Kongo, ɓenezuela da Koriya da Trinidad da kuma Tobago.

Sauran sun haɗa da Masar, Chadi, Indiya, Sudan, Kenya, Zimbabwe, Ethiopia, Indonesiya da Tarayyar Turai da Switzerland da Saudiyya da China da kuma Afirka ta Kudu.

Wata sanarwa da SERAP ta fitar a shafinta na ɗ ranar Litinin, ta yi gargaɗin cewa barin Wike ya ɗauki matakin zai saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma yarjeniyoyin hulɗar diflomasiyya.

“Tinubu ya gaggauta dakatar da Wike daga ɗaukar wannan mataki na son rufe ofisoshin jakadanci 34 a Abuja. Sashe na 22 sakin layi 1 na yarjejeniyar ɓiena ya bayyana cewa ofisoshin jakadanci wurare ne da ba za a iya kutsa musu ba ko take su,” in ji SERAP.

A ranar 26 ga watan Mayu ne, Wike ya ba da umarnin ɗaukar mataki kan gine-gine 4,794 waɗanda ba su biya kuɗin hayarsu ba wanda ya kai na tsawon shekara 10 zuwa 43.

FCTA dai ta ce ofisoshin jakadanci da abin ya shafa za su biya kuɗin tara da ya kai naira miliyan biyu ko uku.

By ukarofi