Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon shugaban Nijeriya, Yakubu Gowon, ya bayyana lokacin yaƙin basasar Nijeriya daga 6 ga watan Yulin 1967 zuwa 15 ga watan Janairun 1970 a matsayin lokaci ma fi wahala a rayuwarsa.
Mista Gowon wanda janar ne na soja mai ritaya, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar bayan karrama shi da lambar yabo ta zama mutum mai ƙima da nasara a taro karo na biyar na mabiya addinin Kiristanci ta Anglican Diocese da ke Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito cewa an yi wa taron take da: “Mutane Masu ƙima: Yin Rayuwa Cikin Gaskiya a Cikin Al’ada ta Yaudara.”
Mista Gowon ya bayyana cewa matakin da ya ɗauka a lokacin yaƙin basasar, bai dauke shi don nuna tsana ba facce domin kare haɗin kan ƙasa a matsayin abun da shi ake bukata.
Ya yi kira ga al’umma da su rungumi gaskiya tare da nuna bukatar yafiya da sasanci da haɗin kai a tsakanin dukkan addinai da kabilu a Nijeriya.
“Kullum sai na tuna da yaƙin basasa. Lokaci ne mafi wahala a rayuwata.”
“Ba shi ne ra’ayina ba, amma dole ce ta sa na yi abin da na yi domin ƙasar nan ta cigaba da zama a dunƙule.”
“Ba na yi hakan ba ne saboda tsana ga wasu mutane ba. Ina da tabbacin haka.”
A yayin da yake tuna baya bayan faruwar lamarin, tsohon shugaban Nijeriya, ya jaddada cewa matakin da ya dauka ya biyo bayan addu’a da riko da gaskiya da tausayawa.
“Idan game da zuciyata ne, duk abin da na yi, na yi ne bayan gabatar da addu’a.”
“Nakan roƙi Allah ya taimake wajen yin daidai gwargwadon yadda yake ganin shi ne daidai cikin ƙauna da mutuntawa ga al’umma.”
“Wannan ce ta sa, a karshe ya mika iya? Kamar yadda suke faɗa ne, ba wanda ya yi nasara, ba wanda ya faɗi,” ya bayyana.
Gowon ya yaba da irin cigaban da Nijeriya ta samu tun bayan yaƙin basasa.
Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su mara wa gwamnati baya a kokarin da take yi na samar da zaman lafiya da ƙauna da mutunta juna.
Shugaban taron, tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, wanda ya samu wakilcin John-Kennedy Opara, tsohon sakataren hukumar kula da masu ziyarar wurin bautar Kiristoci ta Nijeriya, ya taya wadanda aka karrama murna saboda riƙo da gaskiya.
Ya ce, “Waɗannan mutane sun amfani al’umma kuma ta hanyoyi da dama Ubangiji ya yi amfani da su wajen ba wa kasar nan cigaba.”
“Yardar Ubangiji na tare da bayinsa masu jin tsoronsa, Kuma shi ne zai biya su.”
Ya kuma buga misali da littafi mai tsarki na Kirista (25:14) da ya yi kira kan bin daidai da riko da gaskiya ba tare da la’akari da kowanne irin yanayi ba.
Shi ma shugaban coci-cocin Nijeriya (Anglican Communion), Henry Ndukuba, wanda ya jagoranci taron, ya yaba wa waɗanda aka karrama tare da yi in kira ga mabiya addinin Kiristanci da su yi riƙo da gaskiya da nuna ƙarfin guiwa.
Sannan ya yi kira ga Kiristoci da su nuna juriya a wuraren ayyukansu da kasuwancinsu.
“Idan kira ya yi ƙarfi, addini zai ƙarfi, kuma al’umma za ta yi ƙarfi,” ya bayyana.
