Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta taka rawar gani wajen daidaita tattalin arzikin Nijeriya kuma ya yi imanin cewa, gyara ƙasar ba zai yiwu cikin dare ɗaya ba ko da kuwa da karama za a yi amfani. Fayose ya bayyana haka ne a daren Litinin bayan ya ziyarci shugaba Tinubu a gidansa da ke Legas.
A yayin ziyarar, jigo na jam’iyyar PDP, Ayodele Fayose, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan ƙoƙarinsa na ceto Nijeriya daga rugujewar tattalin arziki.
A cewar Fayose, wannan ziyarar ƙashin kai ce kuma ya kawo ta ne don ƙarfafa gwiwar shugaban ƙasar kan ci gaba da inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.
Ziyarar, wanda ta ja hankalin ‘yan siyasa, ta zo ne a yayin da ake fama da rikice-rikice a cikin jam’iyyar adawa ta PDP da kuma yawaitar sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.
Fayose ya bayyana ziyarar a matsayin alamar haɗin kai da sada zumunci a cikin hutun babbar Sallah, yayin da ya sake tabbatar da imaninsa ga shugabancin Bola Tinubu.
Ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai amfani da gogewa wajen mulki da kuma amfani da zurfin tunani wajen magance matsalolin Nijeriya.
Duk da cewa sauye-sauyen Tinubu ba su kawo sakamako nan take ba, amma Fayose ya ce manufofin shugaban ƙasar na kan hanya, kuma za su haifar da abin da ake nema a nan gaba.
Fayose ya yaba wa shugaban ƙasar kan matakan da ya zauka na ƙarfafa tattalin arziki, yana mai cewa waɗannan manufofi sun ba ‘yan Nijeriya yakinin samun sabuwar rayuwa.
Yayin da mutane da yawa suka yi hasashen cewa ziyarar tasa na iya nuna shirin sauya sheaarsa zuwa APC, Fayose ya yi hanzarin musanta irin waɗannan zato.
Tsohon gwamnan ya nanata matsayarsa ta baya, cewa ba zai taba ficewa daga PDP ba duk da cewa matsalolin jam’iyyar sun yi kamari, har kowa ma ya sansu.
Ya ce waɗanda suka sauya sheƙa zuwa APC sun yi hakan ne saboda dalilai daban-daban, ciki har da gamsuwa da aikin Tinubu da kuma rikicin da ke cikin PDP.
ɗan siyasar mai faɗa a ji ya yarda cewa PDP “jam’iyyar na gargarar mutuwa,” inda ya ce tana fama da rikicin cikin gida da aka gaza warwarewa da kuma rashin jagoranci.
“Na faɗa a baya kuma zan sake faɗa: ‘Ranar da na yanke shawarar barin PDP ita ce ranar da zan bar siyasa gaba ɗaya’ “, inji Fayose.
