Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa cire tallafin man fetur da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi ya kafa tarhin kawo ƙarshen taɓarɓarewar tattalin arziki da ya hana Nijeriya asarar sama da dala biliyan 84, ya kuma taimaka wajen gudanar da wasu muhimman ayyuka 40 a faɗin ƙasar nan cikin shekaru biyu.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa ta wallafa mai taken “Bayan Shekaru Biyu: Muhimman Amfanin Cire Tallafin Mai”.
Takardar wadda ta tantance nasarorin da aka samu na cire tallafin tun daga ranar 29 ga watan Mayun 2023, ta bayyana cewa, manufar ta ceci ƙasar daga durƙushewar tattalin arziki a nan gaba, kuma ta bai wa gwamnatin Tinubu damar aiwatar da wasu batutuwan da suka shafi kuɗi na tsawon shekaru da dama, da ƙara yawan kashe kuɗaɗe, da daidaita tattalin arzikin ƙasa.
“Tsakanin shekarar 2005 zuwa 2022, gwamnatocin da suka shuɗe sun kashe dala biliyan 84.39 wajen tallafin man fetur, waɗannan tallafin sun cinye sama da kashi 70 na kuɗaɗen shiga da gwamnatin tarayya za ta iya samu, lamarin da ya jefa ƙasar cikin fatara.
Ya ci gaba da cewa, “Cire tallafin ba wai kawai ya ceci dukkan tattalin arzikin ƙasar daga durƙushewa ba ne, ya kuma ceto wasu jihohi da dama na tarayya daga durƙushewa, a lokacin da wannan gwamnati mai ci ta karɓi mulki, Nijeriya tana kashe kashi 97 na kuɗaɗen shigarta wajen biyan basussuka har sai da adadin bashin da ta ke bi ya wuce tiriliyan N100.
“Tallafin mai ya cinye sama da kashi 70 na kuɗaɗen shigar da gwamnatin tarayya za ta samu, wanda hakan ya tilastawa gwamnatin tsakiya da na jihohi yin amfani da rance mai yawa don kashe kuɗaɗen da suke kashewa a kasafin kuɗinsu, amma cirewar ya taimaka wa ƙasar nan ta ceto biliyoyin kuɗi.”
Har ila yau, ya bayyana cewa galibin jihohin da a baya suke fama da matsalar biyan albashi, sun samu kwanciyar hankali duk da ƙarin albashin da aka yi a baya-bayan nan.
