Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Hada-hadar Hannayen Jari (SEC) ta gargaɗi ‘yan Nijeriya da su guji saka hannun jari a wani cryptocurrency mai suna Punisher Coin, wanda kuma aka fi sani da alamar PUN.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi a Legas, SEC ta ce dandalin ba shi da izini, kuma yana kama da tsarin Ponzi.
Hukumar ta ce, binciken da ta gudanar ya nuna cewa masu tallata dandalin ba su da rajistar yin aiki ta kowace hanya a kasuwar hada-hadar kuɗin Nijeriya.
Sanarwar ta ƙara da cewa “An jawo hankalin Hukumar Tsaro da Kasuwanci zuwa wani dandalin hada-hadar kuɗi mara izini na Crypto da ake kira “PUNISHER Coin”, wanda aka fi sani da “SPUN”, inji sanarwar.
“Hukumar a nan take sanar da jama’a cewa masu tallata shi ko masu ɗaukar nauyin “PUNISHER COIN” wato “SPUN” ba su da rajista ta kowace hanya a kasuwar Nijeriya, haka kuma PUNISHER COIN (PUN) hukumar ba ta amince da shi ba.
“Bincike na farko ya nuna cewa PUNISHER COIN (PUN) dandali ne na Meme, hada-hadar kuɗi na Meme gabaɗaya ba su da wani amfani.
“Haka kuma hukumar tana tunatar da jama’a masu saka hannun jari game da buƙatar ko da yaushe su riƙa samun sahihancin crypto da matsayin rajistar masu tallata su da dandamali na kasuwanci ta hanyar tashar Hukumar: https://home.sec.goɓ.ng/fintech-and-innoɓation-hub-finport/registered-fintech-operators/, ”kafin shiga cikin kowane nau’i na saka hannun jari na dijital.
Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa game da ƙaruwar tsare-tsaren ponzi masu alaƙa da crypto a Nijeriya.
A ranar 1 ga Mayu, hukumar ta gargaɗi ‘yan Nijeriya game da saka hannun jari a kan tofro.com, wani dandali na saka hannun jari mara izini.
A watan Afrilu, wasu ‘yan Nijeriya sun yi asarar kuɗaɗensu bayan da suka saka hannun jari a kasuwar Crypto Bridge (CBEɗ), dandalin ciniki na dijital.
