
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ƴan sanda a Kaduna ta kama mutane guda 13 a yankin Kawo dake jihar, inda wasu ƴan ƙwacen waya suka hallaka jami’in sojan ruwa mai suna Laftanal Kwamado, M. Buba.
Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan ya ce bayan aukuwar lamarin ne jami’ai suka gudanar da atisaye a yankin, lamarin da ya yi sanadin kama mutane 13 da wasu muggan makamai.
Marigayin, wanda ɗaya ne daga cikin manyan ɗaliban kwalejin horar da jami’an sojoji ta Jaji, an daɓa masa wuƙa ne a ƙirjinsa, a madakatar ababen hawa da ke kusa da babbar gadar yankin da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Lahadi.
Hukumar ƴan sanda ta ce, lamarin ya auku ne a lokacin da jami’in ya samu tsaiko a motarsa wanda ta kai ga sai ya canza taya, inda a lokacin da ya fito daga motar da nufin hakan, sai maharan iske shi, sannan suka buƙaci ya ba su wayar salularsa.
Lamarin da ya ƙi amincewa da shi tare da ƙalubalantar su akan haka. Daga nan ne ɗaya daga cikinsu ya daɓa masa wuƙa.
An garzaya da shi Asibitin Manaal ne bayan miyagun sun tsere, inda a nan aka tabbatar da mutuwarsa.
