
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya da dakatar da shirin gudanar da taron addu’a da azumi na kwana uku da nufin samun yalwataccen abinci ga al’umma a ƙasa a sakamakon ƙorafe-ƙorafen da al’umma suka yi wa shirin.
Da fari, Ma’aikatar Noma ta gabatar da shirin domin neman tallafin ubangiji wajen samun kariya ga ɓangaren abincin da kuma ci-gaban ƙasa.
An shirya gudanar da taron ne a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja a ranakun 16, 23 da kuma 30 ga watan Yuni, inda aka gayyaci manyan jami’an gwamnati da wasu ma’aikata zuwa taron, kamar yadda wata takarda daga ma’aikatar ta bayyana.
Daga bisani, bayan samun ƙorafe-ƙorafen al’umma, ma’aikatar ta sake fitar da sanarwar dakatar da shirin zuwa wani lokaci.
Kawo yanzu, ma’aikatar ba ta bayyana dalilin ɗaukar matakin ba game da batun.
