AFMAN ta taya Ahmad Sarari murna bisa samun damar halartar bajekolin finafinai na Toronto da fim ɗin Kakanda

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ƙungiyar Arewa Film Makers Association of Nigeria (AFMAN) ta taya Dr. Ahmad Sarari, shugaba kuma daraktan Sarari Klassique Company Limited, murna bisa nasarar samun gurbin halartar gasar fina-finai ta duniya, Toronto International Nollywood Film Festival (TINFF), da fim ɗin shi mai suna “Kakanda.”

Wannan sanarwar ta fito ne daga shugaban AFMAN NA ƙasa, Salisu Mohammed Officer, wanda ya bayyana farin cikin ƙungiyar da alfahari da irin wannan gagarumar nasara da kamfanin Sarari ya samu.

AFMAN ta bayyana wannan nasara a matsayin shaidar hazaƙa, hangen nesa da jajircewar Dr. Sarari wajen samar da ingantattun fina-finai da ke jan hankalin masu kallo a faɗin duniya. Ƙungiyar ta jinjina wa sadaukarwar da ya yi wajen tabbatar da inganci a harkar fim, lamarin da ba kawai ya bai wa kamfaninsa yabo ba, har ma ya taimaka wajen bunƙasa masana’antar shirya fina-finai a Najeriya, musamman a Arewa.

A ƙarshe, AFMAN ta bayyana cewa nasarar Dr. Sarari wata hanyar ƙarfafa gwiwa ce ga sauran mambobin ƙungiyar. Ta ce kasancewarsa cikin AFMAN na ƙara wa ƙungiyar ƙima, tare da fatan samun ƙarin haɗin gwiwa da nasarori a gaba. Ƙungiyar ta kuma yi masa fatan alheri a ci gaba da tafiyar sa ta harkar fim.

By ukarofi