An rabu dutse a hannun riga a taron APC na Arewa maso Gabas

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Maiduguri

An rabu dutse a hannun riga a sa’ilin gudanar da babban taron jam’iyyar APC wanda ya gudana a Gombe, inda gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisa, da sauran manyan shugabannin jam’iyyar suka halarci taron.

Taron masu ruwa da tsaki na Arewa maso Gabas, ranar Lahadi, rikicin ya kaure ne a lokacin da mataimakin shugaban jam’iyyar a Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu da Shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, suka ki ambato mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima a lokacin da suka bayyana amincewa Shugaba Bola Tinubu ya zarce wa’adi na biyu.

Jaridar Daily Trust, ta ruwaito cewa rikici ya kaure a zauren taron sakamakon rashin ambaton Kashim Shettima a wajen taron inda wasu wakilai da sauran magoya bayan jam’iyyar suka fara ihun tare da barazana ga shugaban jam’iyyar da mataimakinsa a Arewa maso Gabas.

Biyo bayan hargitsewar ɗakin taron, mataimakin shugaban jam’iyyar APC (Arewa), Alhaji Bukar Dalori, ya hau kan dandamalin taron tare da shelanta goyon bayan jam’iyyar kan zarcewar shugaban Kasa Bola Tinubu da Kashim Shettima a wa’adi na biyu tare.

Duk da haka, cece-kucen ya ƙara zurfafa, musamman a lokacin da Dr. Ganduje, a cikin jawabinsa, ya ƙi ya ambaci sunan Shettima tare da Shugaba Tinubu a wa’adi na biyu.

Duk da yadda ya ɗauki dogon lokaci ya na magana na kimanin mintuna 10, Umar Ganduje bai ambaci mataimakin shugaban ƙasa ba, inda hakan ya ƙara wa wutar cece-kucen fetur, al’amarin da ya jawo dole jami’an tsaro suka bashi kariya ta musamman.

Taron ya ƙare dutsi a hannun riga a tsakanin mahalarta taron, sakamakon kaurewar zazzafan cece-kuce a cikin jam’iyyar game da rashin ambaton mataimakin shugaban ƙasa.

Wani bidiyo da gidan talabijin AIT ya nuna ya nuna yadda ake baiwa hamata iska tsakanin mahalarta taron tare da jifan wasu da kujeru.

By ukarofi