Ba a yi wa Arewa wariya a ayyukan Gwamnatin Tarayya ba, inji Ministan Ayyuka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Ayyuka, David Umahi ya yi watsi da ikirarin da ke cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta fifita yankin kudancin Nijeriya wajen aiwatar da ayyukan ababen more rayuwa akan Arewa.

Umahi ya bayyana haka ne a yayin ganawa da manema labarai lokacin ziyarar duba ayyukan titina na kwana biyu a Jihohin Ribas da Bayelsa, inda ya bayyana batun a matsayin abin ruɗarwa.

Ya ce, kimanin kaso 52 na manyan ayyuka a Arewa su ke idan an kwatanta da na kudu mai kaso 48.

Ya kuma bada misali da titunan Sakkwato-Badagry da Kalaba-Abuja da kuma Akwanga-Jos waɗanda duk a Arewa ake yin su.

Haka kuma, Ministan ya zargi masu yaɗa batun da cewa sun ƙirƙiri zantukan ƙarya domin ruɗar da jama’a yana mai cewa gwamnati ta duƙufa wajen yin muhimman ayyuka a kowane sashe na ƙasar ba tare da nuna wariya ga wani ɓangare ko shiyya ba.

A cigaba da jawabinsa, Umhi ya ce ana sa ran kammala aikin titin Bonny zuwa Bodo a Jihar Ribas nan da watan Nuwamban 2025.

Kazalika, ya ziyarci wuraren wasu muhimman ayyuka a sassan jihohin tare da jinjina wa kamfanonin da ke gudanar da ayyukansu duba da yadda ake yin su cikin inganci.

By Babaji