
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu shahararrun jagororin ƴan bindiga da ke ayyukansu a Ƙaramar Hukumar Ɗan-Musa dake Katsina sun ajiye makamansu tare da miƙa wuya ga sojoji da nufin a ba su kariya.
Sannan sun sako wasu mutane guda 16 a ƙarƙashin shirin karɓar tubar ƴan ta’adda da miƙa wuya na sojoji, kamar yadda rundunar sojoji ta bayyana.
A wata sanarwa da ta wallafa a ranar Asabar, rundunar ta ce an yi nasarar haka ne a ƙarƙashin tawagar atisayen FANSAN YAMMA tare da haɗin-gwiwar sauran masu-ruwa-da-tsaki.
Tubabbun ƴan bindigar sun haɗa da Kamulu Buzaru, Manore, Nagwaggo, Lalbi, Alhaji Sani, Dogo Baidu, Dogo Nahalle, da kuma Abdulkadir Black waɗanda suka ajiye makaman nasu ne a ranar 14 ga watan Yuni.
A yayin haka ne kuma suka sako mata guda bakwai da yara tara da ke hannunsu, sannan kuma sun yi alƙawarin sako sauran waɗanda suka yi garkuwa da su a ranar 15 ga Yuni, wato yau kenan.
Tuni aka miƙa waɗanda aka sako ga jami’an ƙaramar hukuma domin damƙa su ga iyalansu.
Haka kuma, sanarwar ta ce an ƙarfafa jami’an tsaro a yankin domin kare dukkan wata tarzoma da ka iya biyowa baya, duba da barazanar tsaro a yankin da shiyyar baki ɗaya.
