Jami’ar ABU ta haramta sanya matsatstsun kaya, shiga ta rashin mutunci da runguma a farfajiyar makaranta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ƙoƙarinta na kare martabar addini da al’adu, Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ta gabatar da sabon tsarin shiga ga ɗalibai da malamai, wanda ya hana su sanya gajerun kaya da ɗamanmu da sanya dogayen gashin gira da kuma runguma a farfajiyar makaranta.

Bayanin hakan na ƙunshe a wata takarda da hukumar gudanarwar jami’ar ta fitar a ranar Litinin, inda ta ce ta yi hakan ne duba da yadda wasu ke yin shiga ta rashin mutunci, wanda a cewarta hakan ya saɓa wa doka da zamantakewar al’ummarta, don haka za a hukunta duk wanda aka samu da laifin saɓa mata.

Takardar ta kuma ce, daga yanzu an haramta wa ɗalibai da malamai sanya matsatstsun kaya waɗanda ba su dace da fagen ɗaukar karatu ba.

Wasu daga cikin kalar kayan da aka haramta sun haɗa da ‘spaghetti straps’, ‘see-through outfits’ wato kayan da ke nuna sassan jikin mutum, wandon jins mai ɗauke da tambura da huji-huji, siket da kuma kayan da ba su kai gwiwa ba saidai idan a yayin wasanni kaɗai, da makamantansu.

Sauran a jaddawalin sune ƴan-kunne ga maza, sarƙar ƙafa da mata ke sanyawa, gashin ido dogo ko mai kala da gyara gashi ta hanyar murza shi ga maza da kuma kitso ga maza.

Haka kuma, ta haramta yin shiga ta rashin kyan gani kamar tara gashi a kai ko gemu mai yawa da ba a kula da shi.

Bugu da ƙari, dokar ta hana yin ababe kamar haka a bainar jama’a: runguma, sumbata da zama akan cinyar juna, sanya tufafin da ke motsa sha’awa, sanya wando iya rabin ƙafa, tabarau mai kala ba tare da izinin likitanci ba da sanya hula hana-salla ta wani salo da ya saɓa wa asalin yadda ake saka ta.

Lamarin ya haifar da suka da cecekuce daga wasu ɗalibai da malamai da ke ganin hakan ya taƙaice musu ƴancin bayyana kai.

By Babaji