‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sanda a Katsina sun sami nasarar ceto mata huɗu daga hannun ‘yan bindiga a ƙauyen Mazare dake ƙaramar hukumar Sabuwa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da haka a wata takardar da ya rabawa manema labarai a Katsina.
Ya bayyana cewa ƴan sandan ƙarƙashin DPO na ƙaramar hukumar Sabuwa suka kai farmaki a ƙauyen Mazare bayan samun bayanan sirri kan ƙoƙarin da ƴan bindigan suka yi na sace waɗannan mata.
Bayan musayar wuta,yan sandan sun sami nasarar ceto matan ciki har da jaririya”DSP Sadiq ya ce.
Sai dai yan bindigan sun raunata mutum biyu cikin mutanen ƙauyen,sun haɗa da Sa’idu Isa ɗan shekara 37 da Sa’idu Wa’alam ɗan shekara 61,inji mai magana da yawun ƴan sandan.
Ya tuni an garzaya da su asibiti suna samun kulawa,su kuma ƴan bindigan sun ranta a na kare.
DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa rundunar ƴan Sanda na nan na ƙoƙarin gano tare da kama ƴan bindigan.
Kwamishinan ƴan sanda a jihar CP Bello Shehu ya jinjina wa jami’an nasa bisa ƙoƙari da ƙwarewa wajen tunkarar ƴan bindiga da har suka sami nasarar ceto matan.
Ya jaddada ƙudirin jami’an ƴan sanda a jihar na kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar.
