Gwamnatin Kano za ta fara shuka bishiyoyi miliyan biyar a jihar 

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano 

Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ta sake jaddada ƙudurinta na shuka bishiyoyi miliyan 5 a faɗin jihar nan a shekarar 2025 da muke ciki.

Kwamishinan ma’aikatar, Dr. Dahir M. Hashim, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyara garin ‘Yan Bawa da ke ƙaramar hukumar Makoda a ranar Talata, a wani ɓangare na bukukuwan Ranar yaƙi da kwararowar Hamada ta bana.

A cewarsa, a garin ‘Yan Bawa, ma’aikatar tana kula da fiye da shukar bishiyoyi 75,000 a matsayin wani ɓangare na kamfen ɗin bishiyoyi miliyan 5 da za a gudanar a 2025.

Kwamishinan ya ce za a yi amfani da waɗannan shuke-shuke wajen faɗaɗa ganuwar bishiyoyi da ke hana yaɗuwar hamada da kuma ƙarfafa garkuwar farko da ke kare ƙasa daga fari da yashi.

Sannan Hashim ya bayyana cewa hamada da fari na barazana ga rayuka da hanyoyin samun abinci, inda ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na da cikakken ƙuduri wajen kare muhalli domin amfanin al’umma a nan gaba.

By ukarofi