Zargin damfarar biliyan N2.5: EFCC ta kama tsohon kakakin majalisar Filato, da wasu 14

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) ta cafke tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Moses Sule, tare da wasu tsaffin ‘yan majalisa 14 bisa zargin karkatar da kuɗaɗe da kuma yin amfani da muƙami.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Kakakin hukumar ya ce jami’an hukumar EFCC na shiyyar Makurdi ne suka kama waɗanda ake zargin a ranar Talata, biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da ‘yan jihar suka yi.

Oyewale ya bayyana cewa, ana zargin tsoffin ‘yan majalisar sun saɓa wa tanadin dokar haramtacciyar ƙasa ta shekarar 2022, sannan kuma suna da hannu wajen badaƙalar sayen kayayyaki.

Ya bayyana cewa sauran ‘yan majalisar da aka kama tare da Sule sun haɗa da Gwottson Fom, Sani Abubakar, Jwe Gwom, Timothy Dantong, Happiness Akawu, da Cornelius Doeyok.

Oyewale ya lissafa wasu da suka haɗa da Agbalak Ibrahim, Danjuma Azi, Fwangje Ndat, Salome Waklet, Namba Rimuyat, Nimchak Rims, Ishaku Maren da Paul Datugun.

“Bincike ya nuna cewa tsaffin ‘yan majalisar sun shafe watanni shida ne kawai a ofis, kuma gwamnatin jihar ta siya musu motocin alfarma da dama a matsayinsu na hukuma.

“Bincike ya ƙara nuna cewa motocin da aka ce kuɗinsu ya kai Naira biliyan 2.5.

“Bayan an tashi daga ofis an so a mayar da motocin ga gwamnatin jihar amma ‘yan majalisar sun tafi da su, kuma duk ƙoƙarin da aka yi na dawo da su ya ci tura.

“Dole ne gwamnatin jihar ta sake siyo wa ‘yan majalisar na yanzu motocin da kuɗinsu ya kai kimanin naira biliyan biyu,” inji shi.

Oyewale ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.

By ukarofi