Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
An bayyana cewa zaratan matasa da aka zaɓo aka ba su horo waɗanda za su taimakawa jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da sauran hukumomi irin su hukumar hana sha da fataucin muggan ƙwayoyi NDLEA da sauransu cewa waɗannan matasa da aka ɗauka don murƙushe matsalar ƙwacen waya da kashe mutane ko illatasu da masu faɗan daba da sauran su gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf zai ba waɗannan matasa masu ƙoƙarin kare mutunci mutanen Kano da addinin su don da zaman lafiyan Kano da kasuwanci Kano masu wannan aiki su 1050 da aka ɗauka don kawo ƙarshen waɗannan matsaloli gwamnan Kano zai ba su goyan baya domin kawar da waɗannan matsaloli da suka addabi al’ummar Kano a wannan lokaci kamar dai yadda kwamishinan tsaron cikin gidan jihar Kano, AVM Ibrahim Umar mai ritaya ya bayyana a lokacin ƙaddamar da dakarun murƙushe faɗan daba da ƙwacen waya da muggan ƙwayoyi a lungu da saƙon jihar Kano da kewaye, wanda aka yi a ranar Lahadi a gidan gwamnatin Kano wanda AVM Ibrahim Umar ya jagoranta a madadin gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Haka kuma ya bayyana cewa wannan aiki na kowa da kowa ne kuma ‘yan bijilante da sauran waɗannan da aka ɗauka aiki doka ta basu damar kama wanda ake zargi da irin wannan laifi don miƙa shi ga ‘yan sanda don haka akwai buƙatar shugabannin al’umma da shugabannin addini da ɗaukacin alummar Kano da masoyan Kano da kowa ya cigaba da addua da bada haɗin kai na ganin an kawo ƙarshen irin wannan matsaloli na faɗan daba, kwacen waya da harkar miyagun ƙwayoyi da sauran su inda kuma ya bayyana takaici akan yadda wasu miyagun ‘yan siyasa ke da hannu wajen haddasa waɗannan matsaloli da ke damun al’ummar Kano a halin yanzu.
A nasa jawabin Janar Gambo Ahmad Mai Adua mai ritaya shugaban kwamitin kawar da harkar miyagun ƙwayoyi da murƙushe faɗan daba da matsalar ƙwacen waya ya ce gwamnan Kano ya damu da wannan matsaloli daga wasu baragurbin matasa da ka aikata irin waɗannan halaye marasa kyau wanda akan hakan ne gwamnan ya bada motoci kimanin 100 domin samun nasarar wannan aiki na murƙushe faɗace faɗacen daba da ƙwacen waya da harkar miyagun kwayoyi da jabun magunguna da waɗanda aikin su ya ƙare wanda babban burin gwamnan Kano taftace Kano da ciyar da ita gaba ta kowanne fanni musamman zaman lafiya, kwanciyar hankali da yalwar arziki a Kano da Nijeriya baki ɗaya.
