Ƙasar Gambiya ta zo Kebbi don neman fasahar noman shinkafa

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Wani ayari daga ƙasar Gambiya ƙarƙashin jagorancin Jakadan ƙasar a Nijeriya Abdoulie Hydara  da kuma babban Sakataren aikin gona na ƙasar Alhagie Nyangado sun ziyarci wata ƙungiyar manoman shinkafar rani mai suna ƙungiyar taimakon kai da kai ta Dankwalli da ke garin Argungu a jihar Kebbi don ganin yadda a ke noman shinkafa.

Da ya ke zantawa da wakilinmu Alhagie Nyangado  ya bayyana cewa ya gamsu da yadda ya ga ana noman shinkafar rani ba tare da wata doguwar wahala ba kuma ana samun abinci mai yawa.

Ya ce ba da dadewa ba ƙasar Gambiya za ta nemi hanyoyin haɗin gwiwa da wannan ƙungiyar ta yadda su ma za su samu irin wannan fasahar da ya ke kusan kashi tamanin daga cikin ɗari na shinkafar da ake amfani da ita a ƙasar suna shigowa da ita ne daga ƙasashen waje saboda haka ne ya sanya su ke  neman ta yadda za su iya noma shinkafar da kan su musamman saboda kasancewar ƙasar su ba ta da yawa.

Da ya ke zantawa da wakilinmu babban Sakatare a ma’aikatar aikin gona ta jihar Kebbi Alhaji Abdullahi Dankawu ya yaba wa ƙungiyar manoma ta Dankwalli bisa ga taimakon kai da kai da kuma jajircewar su wajen aikin noman rani da na damina ba tare da dogara kacokan ga gwamnati ba wanda shi ne silar a zaɓo su daga cikin ƙungiyoyin manoma a matsayin ƙungiyar da za ta karɓi waɗannan baƙin daga ƙasar waje.

Ya kuma yaba wa Gwamna Malam Nasir Idris bisa ga irin tallafi da ya ke bai wa manoma faɗin jihar ta Kebbi.

Shugaban ƙungiyar taimakon kai da kai ta Dankwalli Malam Abubakar Adamu ya bayyana cewa wannan aikin da su ke yi na haɗin gwiwa ne tsakanin manoma ba tare da dogara kacokan ga gwamnati ba.

Mun assasa wannan ƙungiyar ne da zummar taimakon kai da kai sai ga shi yanzu ya kai ga mutanen da ke cikin wannan ƙungiyar sun yi kaɗan suna neman ƙarin mutane da su shigo su rajista don ta tallafa musu da iri da kuma taki don aiwatar da aikin noma.

Ya kuma yaba wa wakilan ƙasar Gambiya da suka yo takakka har wajen su domin su samu fasahar noman shinkafa ta rani wanda kuma in Sha Allahu a shirye su ke da su baiwa ƙasar Gambiya gudummawa a duk lokacin da buƙatar haka ta taso.

By ukarofi