Kwastomomin bankuna sun yi ƙorafin cajis sama da kima ga CBN

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Kwastomomin Bankunan Nijeriya (BCAN) ta ce ta aika saƙon ƙorafi ga Babban Bankin Nijeriya game da yawan cajis da ake cirewa a asusun kwastomomi.

Shugaban BCAN, Uju Ogubunka ya bayyana hakan a ranar Alhamis, a yayin taron fasahar AI da aka shirya da nufin inganta ayyukanta da gamsar da kwastomomi kan harkokin kuɗaɗe a Abuja.

An ɗauki matakin ne a yayin da bankuna suke cazar kwastomomi kuɗaɗen da babu su a cikin waɗanda CBN ya amince da su a hukumance.

A lokacin da ya ke jawabi a taron, Ogubunka ya ce sun rubuta wa CBN takardar ƙorafi domin a samar da mafita ta dindindin ga al’amarin, wanda idan hakan bai samu ba, kwastomomi za su fito da kansu su nema.

Ya kuma ce, tsarin fasahar AI zai ta taimaka wajen magance matsalar cazar kwastomomin sama da kima, yana mai cewa hakan abu ne da ke nuna gaza gamsar da su a yayin harkokin kuɗaɗensu ga bankunan.

By Babaji