Kisan Yelwata: Mazauna ne suka yaudari dakarunmu gabannin harin, inji Babban Hafsan Tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya bayyana cewa dakarun sojoji suna garin Yelwata a Jihar Benuwai ranar 13 ga watan Yuni, 2025, inda aka yaudare su da wani rahoton kai hari na ƙarya daga wani gari dake kusa da yankin, lamarin da ya sa maharan suka yi nasarar hallaka mutane da dama.

Janar Musa ya faɗi hakan ne a yayin hira da manema labarai a Abuja, ranar Alhamis.

Ya ce, a saboda yaɗa batun kai harin na ƙarya a garin dake kusa ya sa sojoji suka mayar da hankali tare da zuwa wajen da aka yi zargin harin.

Ya kuma ce, lallai akwai masu tsegumta wa maharan bayanai akan sojojin da aka tura atisaye.

“Waɗannan mutanen suna ba su bayanai. Suna kai musu abinci. Suna kai musu mata. Wannan shi zai nuna maka yadda al’amarin ya yi muni kuma ya ke da ban-tausayi.”

A makon da ya gabata ne a daren Juma’a wayewar Asabar mahara suka farmaki garin Yelwata, inda suka kashe mutane da dama da ɗaiɗaita sama da 3,000.

Gwamnati ta ce, waɗanda aka hallaka sun kai guda 59 a yayin da wasu ƙungiyoyin ƴancin al’umma suka ce an samu rahoton sama da mutane 200 da aka kashe.

By Babaji