Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta ce ta gano wata sabuwar dabarar satar kuɗi da wasu ’yan siyasa ke amfani da ita a yanzu ta hanyar amfani da ’yan damfara waɗanda aka fi sani da ’yan yahoo a faɗin ƙasar.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede na wannan furuci ne yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Litinin.
Olukoyede wanda ya ce waɗannan matasa ’yan yahoo da suke zubar da kimar Nijeriya a idon duniya sun kuma faɗa dumu-dumu ta’adar nan ta garkuwar da mutane domin neman kuɗin fansa.
Ya bayyana cewa ƙaurin suna da ’yan yahoo suka yi a matsayin miyagu sun shafa wa kowane ɗan Nijeriya baƙin fenti da duk inda suka shiga ake ɗari-ɗari da su a matsayin masu laifi.
Shugaban na EFCC ya ce a yanzu da zarar miyagun ’yan siyasa sun samu damar yin ruf da ciki a kan dukiyar ƙasa, sukan haɗa kai da waɗannan matasa ’yan yahoo-yahoo su ɓoye kuɗaɗen a cikin wani asusun yanar gizo da ake kira wallet.
“Sau tari irin waɗannan ’yan siyasa sukan jibge ’yan yahoo a otel-otel su riƙa buɗe musu asusun ajiya na kirifto su ɓoye biliyoyin kuɗaɗen da suka sata.”
Olukoyede ya buga misali da wani matashi mai shekaru 22 da hukumar ta kama yana yi wa ’yan siyasa irin wannan aika-aikar wanda aka gano ya samu tukwicin Naira biliyan biyar a tsawon watanni 18 kacal.
