Litar fetur za ta iya komawa N1,000 a Nijeriya saboda yaƙin Isra’ila da Iran – Masana

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Masana sun yi gargaɗin cewa yaƙin da ake gwabzawa a tsakanin Isra’ila da Iran zai iya shafar farashin man fetur a duniya kuma hakan zai iya yin illa ga tattalin arzikin Nijeriya.

Masanan na cibiyar Commercio Partners da ke Legas sun  bayyana fargabar ce a cikin wani rahoto da cibiyar ta fitar mai taken: “Farashin kayayyaki ya sauka a Nijeriya a watan Mayu, amma akwai matsala a nan gaba” wanda aka wallafa shi ranar 16 ga watan Yunin 2025.

A cewar rahoton, rikicin da ake fama da shi a yankin Gabas ta Tsakiya zai iya rage yawan man fetur ɗin da ake samarwa a duniya wanda kuma zai kai ga tashin farashinsa a kasuwanni.

Sun yi gargaɗin cewa duk da yake Nijeriya ƙasa ce mai arziƙin man na fetur, amma tashin farashin ba lallai ne ya zama alheri ga ƙasar ba.

Manhaja ta rawaito cewa farashin ɗanyen mai ya riƙa yin tashin gwauron zabo a ’yan kwanakin nan inda ya haura Dalar Amurka 75 kan kowacce ganga.

Sai dai tashin na nufin farashinsa zai tashi a gida Nijeriya, inda farashin zai iya kaiwa Naira 1,000.

A yanzu dai ana sayar da man ne daga tsakanin N870 zuwa N920 a gidajen mai.

“A Nijeriya kuwa, inda yanzu aka janye tallafin man fetur kuma farashinsa ya ta’allaƙa da kasuwar duniya, hakan zai iya shafar tattalin arzikin ƙasar,” inji masanan.

Rahoton ya kuma ce duk da cewa matatar mai ta Dangote na aiki, duk da haka ƙasar ba ta tsira daga barazanar ba.

Ya kuma ce, “Har yanzu shigo da mai ake zuwa Nijeriya, kuma tashin farashinsa a kasuwannin duniya na nufin yadda ake tace shi da rarrabawa ko dakon shi su ma za su ƙaru.

“Idan ɗanyen man ya ƙara tsada, farashin man fetur a Nijeriya, wanda yanzu haka yake wajen N825 zai iya komawa kusan N1,000,” kamar yadda masanan suka yi hasashe.

By ukarofi