Nijeriya ce gaba wajen fitar da fetur daga Afirka a Mayu – OPEC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar ƙasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC) ta ce duk da raguwar fitar da mai da aka samu a Nijeriya, har yanzu ƙasar ce ta fi kowace ƙasa yawa fitar da mai a Afirka.

A cikin rahotonta na wata-wata da ta fitar a ranar Litinin, ƙungiyar ta OPEC ta ce fitar da ɗanyen mai daga Nijeriya ya ragu zuwa ganga miliyan 1.45 a kullum a watan Mayu, daga ganga miliyan 1.48 da aka samu a watan da ya gabata.

Rahoton ya bayyana cewa duk da wannan raguwar, Nujeriya ta ci gaba da zama ƙasa kan gaba a yawan fitar da danyen mai a nahiyar Afirka, inda ta zarce ƙasashen Libya da Aljeriya da Kongo.

OPEC ta ce ta samo waɗannan alƙaluma ne daga bayanan da ƙasashe suka bayar kai tsaye.

OPEC ta ƙara da cewa alƙaluman da aka samu ya nuna cewa Najeriya ta fitar da ganga miliyan 1.54 a kullum a watan Mayu, wanda ya ƙaru daga ganga miliyan 1.52 da aka samu a watan Afrilu.

By ukarofi