Gidauniyar Ɗahiru Mangal ta kashe sama da Naira Miliyan 80 domin yi wa masu lalurar mafitsara aiki a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gidauniyar hamshaƙin ɗan kasuwa kuma shugaban kamfanin sufurin jiragen saman Max da kamfanin simintin Mangal, Alhaji Ɗahiru Barau Mangal ta kashe sama da Naira Miliyan 80 domin yi wa masu ƙaramin ƙarfi da ke fama da lalurar mafitsara aiki kyauta a Katsina.

Ɗaya daga cikin yan kwamitin amintattun gidauniyar Ɗahiru Mangal, Alhaji Hussaini Kabir ya bayyana haka a lokacin da ya ke ƙaddamar da ɗaukar nauyin yi wa masu lalurar aikin a Katsina, yau Asabar.

Alhaji Hussaini Kabir ya cigaba da cewa tun daga fara aikin ga masu wannan lalurar mafitsara zuwa yanzu, an yi wa mutane 3000, wanda sau 10 kenan ana gudanar da wannan aiki ga masu ƙaramin ƙarfi a karo daban-daban, wanda wannan shi ne karo na 10.

Ɗan Kwamitin amintattu gidauniyar Ɗahiru Mangal, Alhaji Hussaini Kabir ya ƙara da cewa a wannan karon, wadda ita ce ta biyu a wannan shekarar, sama da zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan 20, gidauniyar ta ware domin ɗaukar nauyin aikin masu lalurar mafitsara, wanda sama da mutum 100 ne suka amfana.

Haka zalika, akwai cikin masu lalurar da ba su da buƙatar ayi masu aiki, gidauniyar ta ɗauki nauyin ba su duk magunguna da suke buƙata, wanda likitocinmu suka rubuta masu, duk an ba su magunguna kyauta.

Alhaji Hussaini Kabir ya ce wannan ɗaukar nauyin yi wa masu ƙaramin ƙarfi da ke da fama da lalurar rashin lafiya daban-daban na cikin ba da gudummuwar Alhaji Ɗahiru Barau Mangal ga al’ummarsa. Cikin yardar Allah mutane daga lungu da saƙon jihar Katsina da jihohi makwabta da kuma Jamhuriyyar Nijar na tururuwa domin su amfana da wannan taimako. Babban burin wannan gidauniyar shi ne tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi, musamman masu fama da lalurar rashin lafiya daban-daban. Gidauniyar ta tanadi ƙwararrun likitoci da suke tantace marasa lafiya a Asibitin Amadi Rimi da ke ƙaramar hukumar Ɓatagarawa.

Mafi yawancin masu lalurar da aka tattauna da su, sun bayyana jin daɗin su, bisa ga ɗaukar nauyin yi masu aiki lalurar da su ke fama da ita, wadda ba su halin Kuɗin da za’a yi masu aiki, amma yau ga shi kyautar Allah an yi mana, Allah Ubangiji ya saka wa Alhaji Ɗahiru Mangal da kuma jajirtattun masu tafiyar da wannan gidauniyar. Muna kira ga masu hannu da shuni su yi koyi da ayyukan alheran wannan gidauniya, domin tallafawa masu ƙaramin ƙarfi a Jihar Katsina dama ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi