Shugaban Saliyo, Julius Bio ya gaji Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Shugaban ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya zama sabon shugaban Ƙungiyar Shugabannin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), bayan kammala wa’adin jagoranci na Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hakan ya bayyana ne a lokacin taron shugabannin ƙungiyar karo na 67 da aka gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya.

Tinubu ya miƙa ragamar shugabanci ga Maada Bio a gaban sauran shugabanni, saɓanin jita-jitar da ke cewa Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ne zai karɓi jagorancin a wani zama na sirri da aka gudanar kafin taron. Shugaban Saliyo ya yi jawabin rantsarwa inda ya bayyana manyan abubuwan da zai mayar da hankali kansu: farfaɗo da tsarin mulki da dimokuraɗiyya, inganta tsaro a yankin, haɗa tattalin arziki, da kuma gina ingantaccen tsarin ƙungiyar.

Tinubu dai ya fara shugabancin ECOWAS ne a watan Yuli na 2023 a ƙasar Guinea-Bissau, kafin a sake zaɓensa a shekarar 2024 domin ci gaba da aiwatar da manufofin tsaro, sulhu da ci gaba da aka tsara. Shugabannin ECOWAS sun amince da wannan ci gaba domin tabbatar da daidaito da cigaba a harkokin ƙungiyar.

Maada Bio ya sha alwashin ba da fifiko wajen dawo da doka da oda a ƙasashen da suka fuskanci juyin mulki, tare da ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da tattalin arziki a yankin. Ya ce zai yi aiki tuƙuru wajen tabbatar da amincewa da tsarin ECOWAS a idon duniya da kuma rage tashe-tashen hankula da ke ci gaba da barazana ga yankin.

By ukarofi