Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matafiya a Jihar Filato, yana mai buƙatar hukumomin tsaro da su kama waɗanda suka aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da cewa an hukunta su yadda ya kamata. Rahotanni sun bayyana cewa mutane 12 da suka fito daga Zariya, ciki har da mahaifi da ɗan’uwan ango, ne suka rasa rayukansu a harin yayin da suke hanyarsu ta zuwa Jos domin halartar bikin aure.
Shugaba Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin abin ƙyama da rashin imani, yana mai cewa irin wannan ɗanyen aiki ba za a lamunta da shi ba a Najeriya. Ya umurci rundunar ‘yan sanda ta ƙasa da su haɗa gwiwa da sauran hukumomin tsaro da leƙen asiri don cafke duk wanda ke da hannu a wannan mummunan hari. Ya kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankali, yana mai bada tabbacin cewa gwamnati ba za ta zuba ido a ci gaba da zubar da jini ba.
A cikin sanarwarsa, shugaban ƙasa ya ce: “’Yancin yin zirga-zirga na kowane ɗan Najeriya abu ne da ba za a taɓa sassautawa ba. Ba za mu yarda wani ko wata ƙungiya su yi amfani da tashin hankali don hana mutane ’yancinsu na motsi ba.” Tinubu ya buƙaci gwamnatin Jihar Filato da ta ɗauki matakin gaggawa wajen shawo kan irin waɗannan rikice-rikicen da ke faruwa lokaci zuwa lokaci.
Daga ƙarshe, shugaban ya jajanta wa iyalan waɗanda harin ya shafa da kuma gwamnatin jihar Kaduna bisa wannan babban rashi. Ya jaddada aniyar gwamnati ta ganin cewa an kafa daidaito da doka a duk faɗin ƙasar, musamman a sassan da ke fama da rikice-rikicen ƙabilanci da addini.
