
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar jam’iyyar adawa (PDP) ta sake tabbatar da Samuel Anyanwu a matsayin Sakatarenta na Ƙasa.
Shugabanta na riƙon ƙwarya, Ilya Damagum ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai, ranar Laraba.
Damagum, wanda ya samu goyon bayan Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed da tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da wasu masu-ruwa-da-tsaki, ya ce hukuncin ya samu ne a yayin da da dama daga cikin mambobin jam’iyyar suka goyi bayan shigar Anyanwu cikin Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) a jam’iyyar.
Ya kuma ce, an soke taron kwamitin majalisar zartarwar jam’iyyar (NEC) da aka shirya a baya.
A saboda haka ne, PDP ta bakin shugaban nata ta ce za ta a gudanar da babban taron ƴan jam’iyyar, wato ‘extended caucus’ a madadin na NEC da aka soke.
