Rubutu gaba ɗayansa hanya ce ta taskace ilimi – Nasiba Babale 

Spread the love

“Waƙoƙi na sa mutum ya magance matsalar kaɗaici da damuwa”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

A wannan makon shafinku mai farin jini na Adabi ya zanta da wata fitacciyar marubuciyar waƙoƙin turancin nan, ýar Jihar Kano, Nasiba Babale, shugabar ƙungiyar Poetic Wednesday, ƙungiyar da ta tara ɗimbin matasa masu basira da kishin rubuce-rubucen adabi cikin harshen turanci da Hausa. A zantawar da suka yi da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, Nasiba wacce ma’aikaciyar lafiya ce a Babban Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, ta bayyana irin ƙalubalen da marubutan waƙoƙi na zamani ke fuskanta da hanyoyin magance su. Za ku so ku ji irin burin da take da shi a rayuwarta, da yadda ta samu kanta cikin rubutun waƙoƙi. 

MANHAJA: Mu fara da jin cikakken sunanki. Wacce ce Nasiba Babale?

NASIBA: Sunan kenan dai Nasiba Babale. Ni ýar asalin Jihar Kano ce. Marubuciyar waƙoƙin turanci, kuma ma’aikaciyar lafiya. Mai aikin fassara da sana’ar sayar da littattafai. Ni ce shugabar ƙungiyar marubuta waƙoƙin turanci ta Poetic Wednesday. 

Gaya mana wani abu daga tarihin rayuwarki.

An haife ni a garin Kano, kuma a nan na yi karatuna na firamare a makarantar Sheikh Bashir El-Rayyah. Na yi sakandire a makarantar Mairo Tijjani Girl’s Science and Technical College. Daga nan na wuce Jami’ar Bayero ta Kano, inda na karanta fannin kimiyyar gwaje-gwajen ƙwayoyin cututtuka na asibiti, wato Medical Laboratory Science. Yanzu haka kuma ina aiki da asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Waɗanne ƙalubale ki ka fuskanta yayin tasowarki, wanda ya taimaka wajen mayar da ke macen da ki ke a yanzu?

To, gaskiya ba zan iya cewa ga ƙalubalen da ya mayar da ni abinda nake a yanzu ba. Tun tasowata ba ni da wata damuwa. An sanya ni a makaranta, an ba ni dama na yi karatu cikin natsuwa da nasara. Ban nemi wani abu da yaro yake nema na rasa ba. Saboda haka ba zan ce na fuskanci wani ƙakubale a tasowata ba, haka Allah Ya ƙaddara rayuwata cikin nasara har na zama abinda na zama yanzu. Zan iya cewa, ƙarfafa gwiwa, kulawa da yarda, da kuma amincewa da iyayena suka nuna min sun taimaka ƙwarai wajen samun damar da na yi.

Me ya ja hankalinki kan karatu da rubutu?

Ba zan iya cewa ga takamaimen abinda ya janyo ba. Ni dai tun da na tashi na iya karatu na ga ina yi. Na fara da karanta littattafan da mahaifiyata ke da su a gida, da kuma labaru da ke cikin littattafan koyar da turanci na makaranta, wato sashin da ake kira comprehension. Haka nan kawai na taso da sha’awar karanta labarai tun ina yarinya. Na fara rubutu daga ayyukan rubuce-rubuce da a kan bayar a makaranta, wato English composition. Da haka na fara, har daga baya kuma na cigaba zuwa inda nake a yau.

Kina daga cikin mata a Arewa da ake jinjinawa ƙoƙarin su a fannin rubutun waƙen turanci, me ya sa miki sha’awar waɗannan waƙoƙi?

Gaskiya daga karatu ne. Na fara cin karo da rubutacciyar waƙa ta turanci daga wata waƙa da ke cikin littafin turanci na Animal Farm wanda George Orwell ýa rubuta. Daga nan na fara gwadawa nawa rubutun waƙoƙin. Kafin nan na karanta rubutattun waƙoƙin Hausa sosai, amma dai ban taɓa gwada rubutawa ba. Bayan na rubuta waƙata ta farko mai suna Home, sai na nunawa malaminmu na Ingilishi. Lokacin ina ajin ƙarshe a babbar sakandire. Ya ba ni ƙwarin gwiwa sosai. Daga nan kuma akwai wani taro da a ke yi duk ƙarshen wata a Kano, lokacin ina wata ƙungiyar marubuta, wanda sakamakon halartarsa na haɗu da marubuta da dama masu rubutun waƙen turanci, wanda ya sa nima na cigaba da rubuta nawa har na kawo yanzu. Na kan yi mamaki nima, saboda labarai na fara rubutawa, daga baya na juye waƙa.

Ban da rubutun waƙen turanci, wanne abu ne jama’a da dama ba su san kina yi ba?

Ina yin fassara daga Hausa zuwa Turanci, ko daga Turanci zuwa Hausa. Sannan na kan yi aikin tace rubutu. Kuma ni ma’aikaciyar asibiti ce.

Ki kan yi rubutu da Hausa kuwa? Gaya mana rubuce-rubucen ki na Hausa?

Gaskiya na fi yi da turanci. A baya dai na ɗan taɓa waƙen Hausa kamar guda uku haka, amma ban cigaba ba. 

Ba ni labarin littafin kundin waƙoƙin ki na turanci da aka buga, Pickled Moments?

To, shi dai wannan kundi, Pickled Moments, ya ƙunshi waƙoƙi da dama a kan al’amura mabanbanta, wanda na rubuta su a lokuta daban-daban. Akwai waƙoƙi na soyayya, da na tashe-tashen hankula da a ke fama da su a ko’ina a duniya, waƙoƙi akan yaƙin ƙasar Falasɗinu, wasu a kan rikicin Boko Haram da garkuwa da mutane. Akwai kuma waƙoƙi akan al’amuran yau da kullum, al’adu, da sauran su da dama.

Shin kina da shirin buga wani littafin nan gaba?

Gaskiya dai a yanzu babu wani shiri mai ƙarfi a ƙasa.

Mene ne alaƙar ki da ƙungiyar Poetic Wednesday? Me ku ke yi a ƙungiyar?

Da ni a ka kafa ƙungiyar Poetic Wednesdays a shekarar 2016. Kuma a yanzu ni ke riƙe da ragamar jagorancinta. Abinda muke yi shi ne, muna ƙoƙarin raya al’adar karatu da rubutu a tsakanin mazauna yankin arewacin Nijeriya. Ta hanyar shirya tarukan ƙarawa juna sani, tattaunawa, bukukuwan baje kolin fasaha, bayar da kyautar littafi ga yaran makarantu, bayar da horo ga yara a kan rubutu da sauransu.

Wacce gudunmawa ki ke bayarwa don ƙarfafa gwiwar matasa masu sha’awar rubutun waƙen baka?

To, yawanci gudummawar dai ta hanyar ƙungiyarmu ce ta Poetic Wednesdays Initiatiɓe. Wanda na faɗi hanyoyin da muke bi wajen taimakawa masu tasowa a wannan harka. A gefe kuma na kan taimaka ta hanyar shawarwari ga wanda suka nema, da kuma duba rubuce-rubucensu da gyararraki da sauransu.

Wanne tasiri rubutun waƙen turanci yake da shi ga al’umma?

Shi rubutu gaba ɗayansa hanya ce ta taskace ilimi, da adana muhimman bayanai ta cikin waƙe. Yana ankarar da jama’a kan wasu muhimman abubuwa da hankalinsu bai kai kansu ba, don su ɗauki matakin da ya dace, su yi abin da ya kamata, don cigaban kansu ko na al’umma. Waƙoƙi na sa mutum ya magance matsalar kaɗaici da damuwa. Mutane na son karatu ko sauraron waƙoƙin da suke tuna masa da wasu al’amura na rayuwa da suka shafe shi ko al’ummar da yake zaune cikinta. 

Kin taɓa samun wani alheri da ba za ki manta da shi ba a dalilin waƙen da ki ke yi?

Sosai ma kuwa. Abinda na fi tunawa shi ne, a dalilin waƙe na fara shiga jirgin sama. Ka san a wajen talakan Nijeriya wannan abu ne mai muhimmanci. (murmushi). 

Wanne goyon baya ki ke samu daga gida da kuma abokan tafiyar ki maza da mata?

To, Alhamdulillah. Na samu goyan baya daga gida sosai. Tun da mahaifina ya gane ina son karance-karance sai ya dinga sayo min littattafai. Na kan faɗa masa littattafan da nake so,shi kuma yana sayo min su. Har na kai matakin da zan saya da kaina. A yanzu kuma na samu gudunmawa a gida ta bani damarmakin halartar taruka da sauran abubuwa da za su kawo min cigaba. Haka nan sauran mutane da nake mu’amala da su, suna karantawa, su bani shawara, idan da gyara su yi min, sannan kuma su tayani yaɗa rubutuna.

Shin kina ganin akwai wani gata da har yanzu ba a yi wa wannan harka ta waƙen baka a nan Arewa ba?

Sosai ma. Samun masu tallafawa yana da wahala, musamman idan za a shirya taruka haka. Yawanci za ka ga an fi dogara da tallafi daga ƙasashen waje. Gwamnatoci ba su bayar da gudunmawa ga ƙungiyoyi a kan abubuwan da suka shafi rubuce-rubuce. Babu maɗaba’a da suke son buga rubutattun waƙoƙi sosai. Haka nan gidajen jaridu da mujallu babu su da yawa, waɗanda suka buga ɗin ma akasari ba su da halin biyan marubutan.

Wacce shawara za ki bai wa matasa da ke tasowa da son yin waƙen baka a Arewa?

Shawarar ba za ta wuce cewa su yi karatu ba. Waƙe rubutu ne, rubutu kuma daga karatu a ke koyansa. Sannan su dage da rubutun, ko da su na tsoron su na kuskure. Domin da haka ne kawai za su ƙware. Sa’annan su samu wanda za su dinga ba su shawara a harkar, su na duba ayyukansu, domin gyara. Su kuma yi hakuri, domin ba daga fara abu a ke isa in da a ke son zuwa ba. 

Me ya kamata gwamnati ta yi don kawo wa harkar cigaba?

Gwamanti za ta iya taimakawa ta hanyar tallafawa ƙungiyoyi irinsu Poetic Wednesdays, Open Arts, Hill Top Creatiɓe Arts da sauransu a irin shirye-shiryen da suke yi. Haka nan ta hanyar taimakawa maɗaba’o’i masu buga waƙoƙin nan domin adana su ga masu tasowa. Da yawa idan za a yi abubuwa ko bukukuwa da taruka da suka shafi harkar adabi ko waƙa, sai dai ko mutane su yi da aljihun su, ko kuma su yi da tallafin ƙungiyoyi, na ƙasashen ƙetare.

Kina da wani buri na musamman akan wannan abin da ki ke yi nan gaba?

Ina da burin na ga Poetic Wednesdays ta bunƙasa ta wuce inda ta ke yanzu. Ta zama ƙungiyar da ke kan gaba a harkar waƙe a Nijeriya. Haka nan ina da burin na ga The Third Space ta zama babban shagon sayarwa da buga littattafai a arewacin Nijeriya. 

Kina ganin amfani da ingausa wajen rubutun waƙen baka, ya kawo cigaba ne ko cibaya, a tsarin waƙen da ku ke yi?

Shi harshe koyaushe sauyawa yake yi, haka shi ma adabi. Ingausa sabon abu ne, ba zan ce ya kawo cibaya ba, sai dai cigaba, saboda abu ne da yake nuni ga asalin yadda muke magana a rayuwa. Da yawa mutanen dake jin wani harshe fiye da ɗaya, suna yawan cakuɗa harsunan a yayin da suke magana. yana wahala ka yi magana da harshe ɗaya kaɗai na tsawon lokacin ba tare da ka saka wani da ka ke ji ba. Don haka waƙar ingausa haka ne ita ma take. Nuni ce ga yadda muke magana a rayuwarmu ta yau da gobe. Sannan wani salo ne na ƙirƙira da masu hikima kan yi amfani da shi, kamar yadda dama rayuwa ta gada.

To, madalla. Na gode. 

Ni ma na gode ƙwarai da gaske.

By ukarofi