Bisa radin kaina na je ga EFCC, inji Umar Ajiya

Spread the love

Wani tsohon babban jami’in kuɗi, CFO na kamfanin samar da man fetur na Najeriya, NNPCL, Umar Isa Ajiya, ya musanta zargin cewa ta ƙarfin tsiya jami’an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon ƙasa, EFCC suka kama shi ranar Litinin da ta gabata, bisa zargin zamba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, tsohon shugaban sashin kuɗin na kamfanin na NNPC, ya ce saɓanin rahotanni dake kara kaina, shi da kansa ya miƙa kansa ga hukumar, kuma babu wani lokaci da aka kama shi dangane da zargin karkatar da dala biliyan 7.2 na hada hadar kasuwanci a matatar mai na Warri da Fatakwal.

“Babu wanda ya kama ni kan zargin badaƙalar dala biliyan 7.2 dangane da matatar mai, na miƙa kaina babu tilastwa domin amsa tambayoyi ga hukumar EFCC, daga nan kuma na koma gida, saɓanin yadda labarai ke yawo cewa an kama ni bisa zargin zamba” inji shi.

“Na yi aiki a kamfanin NNPC kuma na tafi da mutuncina, babu wanda ya zarge ni da wata zamba a tsawon zamana a Kamfanin, mutanen da ke yaɗa wannan labarin na ƙarya na kamawa da tsare ni kawai suna haka ne domin son su ɓata min suna.”

Mista Ajiya ya ce a shirye yake a kowanne lokaci don kare martabarsa da kuma tsawon shekaru da ya yi a hukumar ta NNPC, inda ya ce, “Ina ƙasar nan kuma a kowacce rana da kuma duk lokacin da EFCC ta buƙaci na bayyana a gabansu zan zo”.

By ukarofi