Daga USMAN KAROFI a Abuja
An kaddamar da haɗakar “Livestock Value Chain for Youth and Women Multipurpose Cooperative Society Limited” a Najeriya domin ƙarfafa matasa da mata, da kuma bunƙasa tattalin arzikin kiwo ta hanyar ƙara darajar kayayyaki da fitar da su ƙasashen waje. An gudanar da bikin ƙaddamarwar ta kafar intanet, inda aka bayyana burin haɗakar na farfaɗo da al’umma, haɓaka ɓangarorin da aka daɗe ana watsi da su, da kuma sauya tsarin kiwo musamman a Arewacin Najeriya.
Shugabar ƙungiyar kuma wadda ta kirkiro da ita, Hajiya Khuraira Musa, ta bayyana cewa kafa ƙungiyar ta samo asali ne daga matsalolin da take gani a cikin al’umma kamar manoma da ke fuskantar ƙalubale, matasa marasa tallafi, da kuma mata masu riƙe iyali ba tare da kayan aiki da yabo ba. Ta ce ƙungiyar na da burin samar da mafita ta hanyar bunƙasa abinci da zaman lafiya.
An kafa kwamitin shugabanci mai ƙarfi da ya haɗa da manyan masana da ƙwararru daga fannoni daban daban kamar harkokin kuɗi, kasuwanci, ayyukan fitar da kaya, ci gaban al’umma da sauransu. Ana sa ran za a cimma buri na samar da kuɗi sama da biliyan huɗu (₦4bn) daga fitar da kayan kiwo zuwa ƙasashen Brazil, Saudiyya, Qatar, UAE da Masar a cikin shekaru uku masu zuwa.
Ƙungiyar ta kuma tanadi shirye shiryen jin ƙai ga al’umma kamar lamuni mara ruwa, tallafi ga ƙananan makiyaya, da kuma ilimantar da mambobi game da kula da dabbobi, dabarun kiwo, lissafin kuɗi, da amfani da fasahar zamani. Hakanan, membobin ƙungiyar za su shiga ta hanyar shawarwarin mambobin da ke da kyakkyawar mu’amala da ƙungiyar, sannan a tantance su kafin amincewa da su a babban taro.
A jawabin ƙarshe, Hajiya Khuraira ta jaddada cewa: “Ba kawai ƙungiya muke gudanarwa ba, muna rubuta sabon tarihi ne na ƙauyukan Najeriya, inda kiwo zai zamo hanya ta zaman lafiya da ci gaba.” Wannan ƙungiya tana da burin zama ƙirar ci gaban ƙasa ta hanyar haɗin gwiwa, fasaha, da tsare tsare na gaskiya da riƙon amana.
