
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis ne Shugaba Bola Tinubu ya gana da Gwamna Siminalayi Fubara, Ministan Abuja Nyesom Wike, Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Ribas da mambobin majalisar.
An yi zaman ne da nufin sulhunta tsakanin ƴan siyasar, wanda Shugaba Tinubu ya jagoranta bisa rikicinsu da ya yi sanadin sanya dokar ta-ɓaci a jihar a ranar 18 ga watan Maris.
Shugaba Tinubu ya yi hukuncin dakatar da gwamnan da ƴan majalisar ne saboda rashin neman hanyoyoyin aiki tare duk da rikicin da ke tsakaninsu da kuma halin tsaro a jihar da suaran su.
Hotunan da aka gani bayan kammala zaman sun nuna cewa an samu sulhunta ƴan siyasar a rikicin nasu da ya ɗauki tsawon lokaci domin kuwa an ga ɗaya daga ciki da ke nuna Tinubu, Wike da Fubara suna murmushi.
Haka kuma, an ga yadda ministan da gwamnan suke tafiya a tare yayin da wasu ƴan majalisar suke biye da su a baya.
Duk da cewa Fadar Shugaban Ƙasa da ɓangarorin biyu ba su yi tsokaci game da zaman ba, ana ganin cewa dokar ta-ɓaci da aka sanya a jihar ka iya zuwa ƙarshe.


