Iran da Isra’ila: Ayatollah Khamenei bai ce uffan ba duk da iƙirarin tsagaita wuta

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Har yanzu shugaban addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Ali Khamenei, bai ce uffan ba, duk da iƙirarin da Amurka ta yi na tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra’ila.

A ranar Litinin ne Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran, wanda ya ce zai kai ga samar da dauwamammen zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu. Sai dai daga bisani, Trump ya nuna damuwa kan yadda ƙasashen Iran da Isra’ila suka ƙi bin ƙa’ida, inda suka kai hari kan junansu.

Shugabannin Iran da wasu manyan jami’ai sun tabbatar da an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninsu da Isra’ila a hukumance. Hakan ya zo ne bayan kwashe kwana 12 ana musayar wuta tsakanin ƙasashen biyu, tun bayan da Isra’ila ta ƙƙddamar da hari na farko a ranar 13 ga watan Yuni.

Matakin da Amurka ta ɗauka na jefa boma-bomai a cibiyoyin nukiliyar Iran ya ƙara ruruta barazanar da aka shiga na fargabar yaɗuwar rikici a faɗin Gabas ta Tsakiya.

Tuni yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara tangal-tangal, inda shugaban Amurka Donald Trump ya zargi dukkanin ɓangarorin biyu da karya yarjejeniyar.

Idan yarjejeniyar ta yi nasara, ana sa ran za ta taimaka wajen cimma zaman lafiya mai ɗorewa. To, amma kamar sauran rikice-rikice, ana buƙatar tattaunawar diflomasiyya mai ƙwari kafin cimma hakan.

Duk da haka, jagoran juyin juya halin addinin Musulunci a Iran, Ayatollah Ali Khamenei, bai ce uffan ba kan wannan sabon mataki na tsagaita wuta da aka cimma. Kamar yadda aka sani, Khamenei ne ke da ikon yanke hukunci na ƙarshe kan muhimman al’amuran ƙasa kuma mutane da dama na jiran matsayarsa.

Rahotanni sun ce, Ayatullah Ali Khamenei ya bar gidansa da ke tsakiyar birnin Tehran. Amma wasu majiyoyi sun ce yanzu haka yana zaune a wani waje daban da tsaro ya kewaye shi. Sai dai, gwamnatin Iran ba ta tabbatar da wannan sauyin matsuguni da Khamenei ya yi ba, ko dalilinsa na barin wancan wuri.

Tun bayan harin da Isra’ila ta kai Iran ranar 13 ga Yuni, ba a sake ganin Khamenei a bainar jama’a ba. Wasu bayanan sirri sun nuna cewa, harin da Amurka ta kai bai tarwatsa muhimman cibiyoyin nukiliyar Iran gaba ɗaya ba.

Ayatollah Ali Khamenei ya gabatar da jawabinsa na farko ga al’ummar ƙasar tun bayan harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar ƙasar a wani ɓangare na yaƙin da ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Iran. Kafar talabijin ta gwamnati Iran ce ta sanya jawabin na Ayatollah da yammacin ranar Alhamis, agogon Tehran.

Cikin jawabin nasa, Khamenie ya ce, “babu wata illa” da ta faru ga cibiyoyin nukiliyar Iran bayan harin da Amurka ta kai a farkon wannan mako.

Sai dai wannan bayani nasa ya ci karo da iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya ce an “lalata” shirin nukiliyar Iran.

Sai dai Imam Khamenei ya ce, “Ina taya ku murna kan nasarar da aka samu akan azzalumar gwamnatin Yahudawa.”

By ukarofi