Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Dakarun Rundunar Operation Haɗin Gwiwa a ranar Litinin ɗin da ta gabata sun yi nasarar daƙile wani mummunan hari da wasu da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne suka kai a ƙauyen Shikarkir da ke ƙaramar hukumar Chibok a jihar Borno.
A cewar Zagazola Makama, ‘yan ta’addan sun afkawa al’ummar garin da misalin ƙarfe 5:20 na yamma, amma sun fuskanci turjiya mai ƙarfi daga jami’an soji, waɗanda ke samun goyon bayan ‘yan sintiri da mafarauta. An gwabza ƙazamin faɗan bindigu wanda ya tilastawa ‘yan ta’addan ja da baya bayan sun samu raunuka da ba a tantance ba.
Abin takaici, a yayin da ake musayar harbe-harbe, wasu fararen hula huɗu sun samu raunuka. Biyu daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su—Ishaku Markson mai shekaru 30 da Buba Zakariya mai shekaru 28—sun rasu ne a babban asibitin garin Chibok.
Sauran mutanen biyun da aka bayyana sunayensu, Yama Wadai mai shekaru 41 da kuma Maina Fali, sun samu raunuka kuma a halin yanzu suna samun kulawa a asibiti. Jami’an kiwon lafiya sun tabbatar da cewa dukkansu suna cikin kwanciyar hankali kuma suna karɓar magani sosai.
