Sojoji sun gama da ’yan ta’addar dake hanyarsu ta ƙaura daga Zamfara zuwa Neja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A wani samame na tsakar dare, dakarun sojojin Nijeriya da ke samun goyon bayan sojojin saman Nijeriya, sun yi nasarar kakkaɓe ‘yan ta’adda da dama da ke yunƙurin yin ƙaura daga jihar Zamfara zuwa jihar Neja ta dajin Kwanar Dutse.

Wannan farmakin da aka gudanar da sanyin safiyar ranar 24 ga watan Yunin 2025, ya yi nasarar daƙile shirin kutsawa da ‘yan ta’addan suka yi a cikin al’ummar Bangi da ke ƙaramar hukumar Mariga, tare da daƙile wani harin da ka iya zama wani babban hari a ƙauyukan da ke kewaye.

Sanarwar da muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanal Appolonia Anele, ya fitar a Abuja, ya ce ‘yan ta’addan da ake zargin sun nufi dajin Kwatankoro ne, ko dai su kafa wani sabon sansani ko kuma su ƙaddamar da hare-hare na haɗin gwiwa kan al’ummomi masu rauni a yankin.

Rundunar sojin Nijeriya ta ce, sojojin sun yi gaggawar tunkarar ‘yan ta’addan a wani ƙazamin musayar wuta da aka yi a tsakar dare da aka shafe sama da sa’o’i uku ana yi. Mummunan faɗan ƙasan ya tilasta wa ‘yan ta’adda cikin ruɗani ja da baya.

Ta ce daga bisani an tura jiragen sojojin sama domin kai sahihan hare-hare ta sama kan hanyoyin tserewar su, wanda hakan ya yi sanadin yin ɓarna ga maharan da ke tserewa.

“Ko da yake har yanzu ba a tabbatar da adadin ‘yan ta’addan da aka kashe ba, hanyoyin jini da yawa a kan hanyoyin tserewar na nuna asara rayuka,” inji majiyoyin soja.

Duk da nasarar da rundunar ta samu, rundunar ta tabbatar da cewa sojoji 17 ne suka rasa rayukan su a yayin arangamar, yayin da wasu 10 suka samu raunuka daban-daban. An kwashe ma’aikatan da suka jikkata zuwa asibitin sojoji kuma an ce suna cikin ƙoshin lafiya.

Da yake mayar da martani kan wannan ci gaba, babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Oluwafemi Oluyede, ya nuna matuƙar alhininsa kan rasa sojojin, inda ya bayyana su a matsayin jarumai da suka mutu wajen kare martabar Nijeriya.

Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansu tare da bayar da agajin gaggawa da kula da lafiyar sojojin da suka jikkata.

“ƙudirinmu na kawo ƙarshen ta’addanci da kuma maido da zaman lafiya a kowane ɓangare na Nijeriya ya kasance kan gaba, rundunar sojojin Nijeriya tare da haɗin gwiwa da sojojin ruwa, sojojin sama, da sauran jami’an tsaro za su ci gaba da farautar ‘yan ta’adda da gungun masu aikata laifuka a faɗin ƙasar nan,” inji Janar Musa.

Ya kuma buƙaci jama’a da su kasance masu taka-tsan-tsan tare da ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da bayanan da za su taimaka wajen kawar da barazana da kare al’umma.

Rundunar Sojin Nijeriya ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya ƙudirin ta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, inda ta jaddada cewa sadaukarwar da jaruman da suka mutu suka yi ba zai faɗi ƙasa banza ba.

By ukarofi