Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
ƙungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya (ACF) ta yi Allah-wadai da kisan gilla da aka yi wa wasu mutane 13 da suka halarci ɗaurin aure a garin Mangun da ke ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato, inda ta bayyana harin a matsayin wani hari da gangan da kuma cin zarafi kan wasu ‘yan ƙasa da ba su ji ba ba su gani ba, bisa la’akari da addini.
Waɗanda aka kashe ɗin waɗanda akasari ‘yan asalin garin Zaria ne a jihar Kaduna, an ce suna kan hanyarsu ta zuwa ƙaramar hukumar ƙuan’pan ne domin bikin aure a ranar 20 ga watan Yuni, inda aka kai musu hari bayan sun tsaya neman hanya da misalin ƙarfe 8:00 na dare.
A cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta na ƙasa Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ACF ta bayyana lamarin a matsayin wani al’amari mai tada hankali na hare-haren ƙabilanci a kan matafiya a jihar Filato.
Taron ya bayyana cewa bayanai daga bakin waɗanda suka tsira sun nuna cewa an yi wa waɗanda aka kashe ɗin ƙawanya ne da gangan kuma aka kashe su.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ba yau aka fara kashe matafiya da ba su ji ba ba su gani ba a jihar Filato, an daɗe ana yi,” inji sanarwar, inda ta yi nuni da bala’o’in da suka faru a baya da suka haɗa da kisan matafiya 26 da suka dawo daga Bauchi a watan Agustan 2021 da kuma kisan wani babban jami’in soja a shekarar 2018.
ƙungiyar ta zargi gwamnatin jihar Filato da gazawa wajen tabbatar da adalci a shari’o’in da suka gabata, inda ta bayyana cewa har yanzu waɗanda suka kashe jami’in sojan na tafiya cikin ‘yanci duk da alƙawuran da aka ɗauka.
Ta kuma nuna damuwa cewa kisan na Mangun na iya kasancewa wani lamari da za a yi watsi da shi idan hukumomin tsaro na tarayya suka gaza magance shi.
Yayin da take amincewa da alƙawarin da gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya yi na gurfanar da waɗanda ke da hannu a kashe-kashen na baya-bayan nan—wanda aka ruwaito ana tsare da mutane 22 a gidan yari, ACF ta buƙaci hukumomin tsaro na tarayya su gudanar da bincike mai zaman kansa.
Ta ƙara da cewa, dole ne gwamnatin tarayya ta ɗauki cikakken ikon binciken domin tabbatar da gaskiya da kuma kaucewa son zuciya.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Tarihin gwamnatin jihar Filato na magance irin waɗannan bala’o’i ba ya ƙarfafa kwarin gwiwa.”
“Matsakaicin tsaka-tsaki da yanke hukunci na tarayya ne kawai zai iya dawo da adalci da kuma daƙile hare-hare na gaba.”
Taron ya yi gargaɗin cewa matsalar rashin tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a faɗin arewacin Nijeriya na haifar da babbar barazana ga haɗin kan ƙasa, tattalin arziki da zamantakewar al’umma.
Ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta yi wa tsarinta na tsaro garambawul tare da tunkarar duk wani mai tayar da hankali da hannu mai tsauri.
Taron ya kuma yi kira ga malaman addini, sarakunan gargajiya, da ƙungiyoyin farar hula da su ƙara ƙaimi wajen tattaunawa a tsakanin al’umma, sulhu, da samar da zaman lafiya, tare da gargaɗi kan illolin da ke tattare da tashin hankali da kuma taka tsan-tsan da adalci.
ACF ta nanata ƙudurinta na ganin an samar da dunƙulewar Nijeriya bisa adalci da mutunta juna, sannan ta jajantawa iyalan waɗanda lamarin ya shafa, tare da yin kira da a gaggauta yin adalci a bayyane.
