Bayan shekaru 21, Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan tsofaffin ma’aikatan ‘Nigeria Airways’ kuɗaɗensu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Biyo bayan jinkiri na tsawon sama da shekaru 20 tsofaffin ma’aikatan kamfanin ‘Nigeria Airways’ da aka rushe za su karɓi kuɗaɗen fanshonsu, yayin da Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci Gaban Sararin Samaniyar Nijeriya, Festus Keyamo ya amince da biyansu haƙƙoƙin nasu.

Lamarin da ya zama gagarumar nasara a tarihin harkar sufurin jiragen sama na Nijeriya tun bayan rufe kamfanin a ranar 30 ga watan Satumbar 2004.

Da dama daga cikin ma’aikatan sun rasu, yayin da masu rai acikinsu suke rayuwa a halin aunci wajen jiran a yi musu adalci da biyansu kuɗaɗensu.

An sanar da amincewar ne a sakatariyar hedikwatar ƙungiyar manyan jami’an sufurin jiragen sama ta ƙasa (ATSSSAN) a Legas, a yayin wani taro.

Haka kuma, an bayyana lamarin a matsayin nasarar samun adalci da juriya ga Shugaban ƙungiyar Aɓiation Union Grand Alliance (AUGA), Kyaftin Shuaibu Alfa.

Ya kuma yaba wa ministan bisa jajircewarsa wajen ganin an saurari kokensu tare da tabbatar musu da samun nasara.

By ukarofi