Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A wani al’amari mai ban mamaki, Femi Soneye, mai magana da yawun Kamfanin Kula da Harkokin Man Fetur ta ƙasa (NNPCL), ya yi murabus, bisa zargin rashin jituwar da ake samu a ɓangaren hukumar gudanarwar kamfanin.
Majiyoyin da ke kusa da lamarin sun shaida wa jaridar News Point Nigeria cewa dangantakar Soeye da sabbin shugabannin ta kasance cikin tashin hankali tsawon makonni.
Rahotanni sun ce rikicin ya ta’azzara ne bayan hukumar gudanarwar ta zarge shi da fallasa wasu muhimman bayanai dangane da labarin ‘Retreat’ na Rwanda ga Sahara Reporters.
Ruwanda Retreat, babban taron da ya tada sha’awar jama’a da siyasa, ya kasance batun cece-kuce a cikin NNPC.
Zargin da hukumar ke yi na hannun Soeye a cikin shelar ya haifar da ƙara rashin yarda da zargin rashin aminci.
Baya ga damuwar da aka samu kan wannan fallasar, sabbin shugabannin kamfanin na NNPC sun soki Soneye kan abin da suka bayyana a matsayin rashin kula da kuɗaɗen kafafen yaɗa labarai.
Ana zargin cewa an karkatar da kasafin kuɗin kafafen yaɗa labarai da ke ƙarƙashin sa ba tare da wani cikakken bayani ba, lamarin da ya haifar da ayar tambaya game da gaskiya da riƙon sakainar kashi a ɓangaren sadarwa na kamfanin.
Yayin da yake tabbatar da murabus ɗin nasa a wata sanarwa da Soeye ya fitar a ranar Asabar da ta gabata kuma ya miƙa wa News Point Nigeria., Soneye ya ce murabus ɗin nasa zai ba shi damar mayar da hankali kan harkokin kasuwanci.
“Ina miƙa godiya ta a gare ku gaba ɗaya saboda goyon baya maras iyaka, ƙwarewa, da kuma jajircewa na gaske da kuka nuna wajen taimakawa wajen tsarawa da faɗaɗa labarin NNPC cikin watanni 20 da suka gabata.
“Gudunmawarku na gina ingantaccen sadarwa mai inganci ga kamfanin samar da makamashi na ƙasa babban abu ne.
“Ina so in sanar da ku cewa na yi murabus daga matsayina na Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin NNPC.
“Wannan shawarar za ta ba ni damar ba da ƙarin lokaci ga iyalina da kuma gudanar da ayyuka na kaina waɗanda yanzu ke buƙatar kusanci na.
