’Yan kasuwa za su shiga shirin Ɗangote na rabon fetur kai tsaye

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar ’Yan Kasuwar Man Fetur ta Nijeriya (MEMAN) ta ce za su tattauna da matatar man Dangote domin fahimtar shirinta na samar da mai kai tsaye ga gidajen mai a faɗin ƙasar.

Sakataren Zartarwa na ƙungiyar MEMAN, Clement Isong ne ya bayyana haka a wani taro ta intanet da ƙungiyar ta shirya a ranar Alhamis.

Isong ya yi nuni da cewa, ‘yan kasuwar za su kuma yi hulɗa da Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nujeriya da sauran masu ruwa da tsaki yayin da suka ɗauki lokaci wajen fahimtar sabon tsarin matatar Dangote.

“A wannan lokacin, muna kallon kasuwar, muna ƙoƙarin fahimtar ta, mun karanta ta a cikin labarai, muna buƙatar mu fahimci ainihin inda ak dosa da kuma abin da yake tasiri kafin mu tsunduma.

“Kuma hakan na buƙatar tattaunawa da yawa, tattaunawa da Dangote da kansa, tattaunawa da hukumomi, tattaunawa da sauran masu ruwa da tsaki, a wani lokaci, za mu shiga tare da yin abin da ya dace don kare kasuwa idan har ya zama dole mu yi hakan, amma a yanzu muna ƙoaarin fahimtar ainihin mene ne wannan shiri da kuma yadda zai yi tasiri a kasuwa.

Sai dai Isong ya bayyana cewa shirin da Dangote ya yi na raba man fetur da motocin dakon iskar gas ya yi kyau, duk da cewa babu isassun kaya.

“Shirin CNG manufa ce ta gwamnati. Yana da manufofin da har yanzu ake aiwatarwa. Ba mu da isassun kayayyakin more rayuwa na CNG. Don haka, dole ne a yi shiri mai kyau don samun damar aiwatar da shi. Kamfanoni masu ƙarfi ne da za su yi amfani da damar da ake da su,” inji shi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne matatar mai ta Dangote ta bayyana shirin fara rabon man fetur kai tsaye zuwa gidajen mai da sauran masu ruwa da tsaki a faɗin ƙasar nan. Za a fara shirin ne a ranar 15 ga Agusta tare da sabbin manyan motocin dakon mai 4,000.

By ukarofi