
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN) ya sanar da cewa ya yi nasarar caza sababbin manyan tiransfomomi guda biyu na tashar da ke da nauyin 330/132/33kV a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi.

Lamarin da ya yi sanadin ƙara ƙarfin lantarki da bunƙasa shi a shiyyar.
Mai magana da yawun Kamfanin, Ndidi Mbah a wata sanarwa, ya ce an gudanar da aikin ne a rana Juma’a da misalin ƙarfe 1 zuwa 3 na rana.
Ya bayyan cewa, hakan da aka yi ya yi sanadin samuwar ƙarin megawat daga 300 zuwa 450 a rumbun shiyyar.

Haka kuma, a sakamakon haka ne Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Kaduna ya samu ƙarin megawat 120 ga kwastomominsa a Kebbi, Sakkwato da kewaye.
Sannan, al’amarin zai haifar da samun ƙarin adadin bada wuta mai yawa ga Niamey a Jamhuriyar Nijar.
Daga ƙarshe, Mista Mbah ya ce suna aiki tuƙuru wajen cigaba da faɗaɗawa da kula da ɓangaren raba wuta a Nijeriya tare da tabbatar inganta harkokin gudanarwa.

