Kebbi: ‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da makamai bayan farmakar ofishin ƴan sanda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da cewa, wasu gungun ƴan bindiga sun farmaki wani ƙaramin ofishin jami’an ƴan sanda dake Makuku a Ƙaramar Hukumar Zuru, inda suka tsere da wasu bindigogi.

Daraktan tsaro na gwamnatin, Abdulrahman Zagga ya bayyana hakan ga manema labarai, ranar Asabar.

Ya ce, ofishin, wanda galibin jami’an wajen ƴan aikin wucin-gadi ne, yq gamu da iftila’in ne daga wasu dandazon ƴan bindiga, waɗanda suka yi ba-takashi da jami’an, lamarin da ya yi sanadin lallasa ƴan sandan duba da ƙarfin yawansu.

“Ƴan bindigar sun ƙone wata motar sintiri ƙirar Toyota Hilux na ofishin, sannan suka tsere da wasu bindigogi da ba a bayyana adadinsu ba.”

Zagga ya kuka ce, a yayin da aka samu labarin harin ne sai gwamnatin ta nemi agajin gaggawa daga rundunar sojojin sama, lamarin da ya sa ƴan bindigar suka ja da baya.

Ya ƙara da cewa, babu asarar rai ko jin rauni a harin, sannan galibin ƴan bindigar sun shigo musu ne daga jihohin Zamfara da Neja, yana mai cewa iyakar da jiharsu ta yi da Neja tana taimakawa wajen sauƙaƙe wa ƴan ta’addar kai ire-iren harin.

Kazalika, ya ce ba kamar sauran jihohi ba, jihar ba ta da wata yarjejeniyar sulhu tsakaninta da wata ƙungiyar ƴan bindiga ko jagororinsu.

By Babaji