Yadda rufe iyakokin ƙasashen Benin da Nijar ya kawo wa Kwastom rashin kuɗin shiga

Spread the love

ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rufe kan iyakokin ƙasar Benin da ƙasar Nijar ya kawo wa hukumar kwatsam ta Najeriya rashin samun kuɗaɗen shiga musamman a ofishin ta da ke iyakokin Arewacin ƙasar Nijeriya.

A Jihar Katsina lamarin ya fi ta’azzara domin hukumar ta dogara wajen samun kuɗin shiga ta hanyar shigar da kaya zuwa Nijeriya ta kan iyakokin ƙasar Nijar zuwa Nijeriya.

Bugu da ƙari wasu ƙarin matakai da hukumomin ƙasar Nijar suka ɗauka kan dangantaka da Nijeriya suma sun kawo babban matsala ga hukumar kwastam wajen samar da kuɗaɗen shiga.

To sai dai hukumar a Jihar Katsina ta cigaba da wayar da kan jama’a musamman al’ummomi da haɗin gwiwar jami’an tsaro da ke aiki a kan iyakokin jihar game da illar fasa ƙwauri da safarar bil’adama domin aikin bauta da safarar miyagun ƙwayoyi a tsakanin ƙasashen.

Manyan jami’an hukumar ƙarƙashin kwanturola Idris Abba Aji mai kula da Jihar Katsina suka jagoranci zaman tattaunawa a kan iyakar Magamar Jibiya.

Haka kuma zaman ya sami halartar jami’an sojoji,ƴan sanda, jami’an hukumar tsaron farin kaya na Civil defence da jami’an hukumar shigi da fici.

Kwanturola Abba Aji ya kuma buɗe tashar kan ƙasa a garin Funtua wanda ya bayyana cewa buɗe wannan katafararen tasha zai samar da aikin yi ga matasa da kuma bunƙasa ƙananan sana’o’i a yankin.

By ukarofi