Majalisar dokokin Katsina za ta tantance tsoffin jami’an tsaro da za su kula da hukumar tsaron al’umma

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Majalisar dokoki ta Jihar Katsina za ta tantance wasu tsaffin jami’an tsaro su uku da gwamnatin Katsina ta aikewa majalisar da za su kula da hukumar tsaron al’umma ta jihar (CWC).

Shugaban masu rinjaye na majalisar Hon Shamsuddeen Abubakar Dabai ya karanta takardar buƙatar tantance jami’an tsaron.

Sunayen tsaffin jami’an tsaron da gwamnati ta tura wa majalisar sun haɗa da Manjo Junaidu Bindawa mai ritaya matsayin shugaba,Sadiq I Kaita a matsayin mataimaki da laftanar kanal Suleiman Sayaya a matsayin mamba.

Haka kuma ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ɗandume Hon Yahaya Nuhu Mahuta ya buƙaci gwamnatin Jihar Katsina da ta amshi makarantar sakandare ta al’umma da ke garin Ɗandume domin bunƙasa harkokin ilmi a yankin.

Shima ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kusada Hon Ghali Garba ya gabatar da ƙudirin buƙatar gina hanyoyin ruwa a cikin garin Yashe domin magance yaduwar zaizayar ƙasa da kwararowar hamada a yankin.

Bayan karanta ƙudurorin daga karshe majalisar ta amince da su,inda nan take kakakin majalisar Rt Hon Yahaya Daura ya umarci akawun majalisar da ya turawa ɓangaren zartarwa domin ɗaukar matakan da ya dace.

By ukarofi