
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yayin wani ba-takashi da aka yi a tsakanin dakarun tsaro da ƴan bindiga ne aka yi nasarar halaka Yello Ɗan-Bokolo, wanda ɗan uwa ne ga Bello Turji.
An kuma kashe wasu ƴan bindiga da dama a yayin gumurzun, wanda aka yi a Ƙaramar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara.
Ɗan-Bokolo, wanda rahotanni sum bayyana cewa ya fi Turji rashin tausayi, ya rasa ransa ne a sakamakon raunukam da ya samu a ƙarshen mako, wanda aka yi jana’izarsa a ranar Asabar da ta gabata.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, mazauna sun ce aƙalla ƴan bindiga 170 aka halaka tare da kwamandansu.
Rundunar ƴan sanda ba ta fitar da wani rahoto kan al’amarin ba, saidai kakakinta na jihar, Yazid Abubakar ya ce za su fitar bayan kammala bincike a kai.
Al’umma a yankin Gundumar Kurya na Ƙaramar Hukumar sun yi murna da kisan ɗan bindigar da ƴan dabara duba da yadda ya addabe su na tsawon shekaru.
