An yi addu’ar kwana bakwai da rasuwar mahaifiyar Babban Editan jaridar Daily Trust

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

Dafifin al’ummar musulmi ne da suka fito daga sassa daban-daban na rayuwa, suka halarci addu’ar kwana bakwai da rasuwar mahaifiyar Babban Editan jaridar Daily Trust, Hajiya Rabi Idris, a gidan su da ke Tudun Faira a Jos.

Bayan an yi saukar Alƙur’ani Mai Girma, da addu’o’i daga manyan alarammomi da suka halarci taron addu’o’in daga sassa daban-daban na Jos, Alaramma Hamisu Umar ya yi addu’ar ubangiji Allah ya gafarta mata zunubanta, ya kuma sa jinyar da ta yi ta zama kaffara gareta. Ya yi fatan ubangiji Allah ya cigaba da haɗa kan zuriyar da ta rasu ta bari, Ya ƙara albarka a rayuwarsu baki ɗaya.

Shi ma Babban Editan, Hamza Idris, wanda ya kasance a wajen taron addu’o’in tare da sauran ýan’uwansa, ya yi wa jama’a godiya da irin ƙauna da kulawar da suka nuna masa, musamman yadda wasu suka je har Kano inda ta rasu, suka yi masa ta’aziyya, da iyalinta baki ɗaya. Ya kuma yi godiya da irin ɗimbin addu’o’in da ake yi mata, har kawo yanzu.

Marigayiyar ta rasu ne a ranar 23 ga watan Yuni, a gidanta da ke Ɗorawar ‘Yan kifi, a Rijiyar Zaki cikin garin Kano. Ta rasu tana da shekaru 75 ta bar ýaýa 11 da jikoki 44.

Muna addu’ar Ubangiji Allah ya haskaka makwancin ta, ya kuma sada ta da ceton shugaban halitta, Annabi Muhammad (SAW).

By ukarofi