
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta shirya sauraron sabuwar buƙatar da Tukur Mamu ya shigar, wanda ake zargin sa da zama wakilin tattaunawa na ƴan ta’adda a lokacin da suka farmaki matafiya a jirgin ƙasa akan hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Abuja a watan Maris, 2022.
Alƙali Mohammed Umar a yayin zama a kotun ranar Litinin, ya ce za saurari buƙatar belin nasa ne a ranar 22 ga watan Yuli.
Lauya mai kare Mamu Johnson Usman (SAN) ya nemi a ɗage batun a ranar Litinin domin ya samu damar yin nazari game da takardar ƙalubale da lauyan da ya shigar da ƙara David Kaswe ya gabatar masa.
A ranar 7 ga watan Satumbar 2022 aka kama Mamu wanda aka tsare shi a hannun ƴan sandan farin kaya na SSS bisa zargin sa da alaƙa da ƴan ta’adda.
Kimanin mutane takwas ne suka rasu a yakin harin yayin da wasu 168 suak ɓata waɗanda ake kyautata zaton an yi garkuwa da su ne.
