MOPPAN ta yi tir da kalaman Al-Hikima na sukar ƴan Kannywood

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Ƙasa (MOPPAN) ta yi alla-wadai da kalamai marasa daɗi da wani Abdullahi Al-Hikima da ke sayer da maganin gargajiya ya yi akan ƴan masana’antar fina-finai ta Kannywood.

A sanarwar ta Babban Sakataren ƙungiyar, Dakta Mohammed Ibrahim Gumel ya fitar, MOPPAN ta ce lallai mai maganin ya ci zarafinsu duk da cewa su ne silar shahararsa a duniya.

Ta kuma bayyana shi a matsayin mara kunya, mutunci da yakana gami da saurin manta alheri da masana’antar ta yi masa.

Akan hakan ne ƙungiyar ta yi jinjina ga waɗanda suka bayyana fushinsu game kalamansa nasa daga cikin ƴan masana’antar da waɗanda suka nemi a yi watsi da shi da lamarinsa.

MOPPAN har’ilayau, ta yaba wa al’umma bisa yadda suka nuna rashin goyon bayansu ga mai maganin da yi masa martani masu zafi.

Kazalika, ta yi godiya ga gwamnatocin Nijeriya da na jihar Kano tun daga ta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ta Bola Tinubu da ma’aikatansu da kuma ɗaukacin ƴan Kannywood da masu nufinta da alkhairi.

Haka kuma, ta yi kira ga ƴan masana’antar da su riƙa hattara da waɗanda za su riƙa mu’amalanta ko janyo su a jiki, tana mai cewa ba za ta lamunci cin mutunci ba daga kowaye.

By Babaji