Jam’iyyar APC reshen Zamfara ta bayyana ƙwarin gwiwa ga muƙaddashin shugaban APC na ƙasa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Hon. Tukur Umar Ɗanfulani ya taya Hon Ali Bukar Dalori murna bisa naɗin da aka yi masa a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa, inda ta bayyana shi a matsayin shugaban jam’iyyar da zai kai jam’iyyar zuwa ga cin nasara.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar Yusuf Idris ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau yau Laraba.

“Naɗin shaida ne cewa jagoran jam’iyyar na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, shugabannin jam’iyyar, jiga-jigan jam’iyyar, mambobinmu da kuma ɗimbin magoya bayanmu suna da tabbaci, da ƙwarin gwiwa ga sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa, wajen tafiyar da al’amuran jam’iyyar yadda ya kamata “.

Jam’iyyar ta yi addu’ar Allah ya yi masa jagora ya kuma kare tare da kawo sauyi ingantacce don ciyar da jam’iyyar APC gaba.

“Haƙiƙa harkokin tafiyar da jam’iyyar tun daga shugabanin jihohi, mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa har zuwa sauran shugannin jam’iyyar APC za su shaidi sauyin da sabon Slshugaban jam’iyyar na ƙasa zai kawo domin cimma sabbin manufofin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.” Yusuf yace

“A madadin Shugabanni, Dattawa, SWC, da magoya bayan jam’iyyar a dukkan matakai a Jihar Zamfara, muna da yaƙinin sabon Shugaban jam’iyyar na ƙasa zai ciyar da jam’iyyar gaba domin cimma nasara a tsawon lokacin shugabancin shi”.

Jam’iyyar ta kuma bai wa muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa tabbacin mara masa baya domin samun nasara.

By ukarofi