
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan wasan ƙasar Portugal da Liverpool, Diogo Jota ya rasa ransa a hatsarin mota yana mai shekaru 28 a duniya.
Haka kuma, ɗan uwansa Andre Silve ya rasu a hatsarin, wanda ya faru a yankin Zamora ta ƙasar Sifaniya.
Rahotanni sun bayyana cewa, motar tasu wadda ƙirar Lamborghini ce, ta samu iftila’in ne a lokacin da ta yi yunƙurin wuce wata mota, inda ɗaya daga cikin tayoyinta suka fashe, lamarin da ya yi sanadin wuta ta kama motar.
Jota, auri Rute Cardoso ne a watan da ya gabta bayan shafe tsawon lokaci suna tare, inda suka haifi ƴaƴa uku a tare.
Ya kuma taimaka wa ƙungiyar Liverpool wajen lashe gasar Premier League na kakar wasan da ta gabata.
Sannan, yana ɗaya daga cikin ƴan wasan Portugal a suka lashe Nations League akan Sifaniya a watan Yuni.
